✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban majalisar malamai ba shi ne shugaba na koli a kungiyar Izala ba -Malam Albani

Shugaban matasa na kasa na kungiyar Izalatul Bid’a Wa Ikamatus Sunnah, Malam Muhammah Jamil Abubakar Albani ya kalubalanci wadanda suke adawa da shugabancin Shaikh Bala…

Shugaban matasa na kasa na kungiyar Izalatul Bid’a Wa Ikamatus Sunnah, Malam Muhammah Jamil Abubakar Albani ya kalubalanci wadanda suke adawa da shugabancin Shaikh Bala Lau su nuna inda kundin tsarin dokokin kungiyar ya ce shugaban majalisar malamai, Shaikh Sani Yahaya Jingir ne shugaban kungiyar Izala na koli.
Malam Albani, dan asalin garin Zariya da ke Jihar Kaduna, ya yi furucin haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon jiya yayin da shugabannin matasa na kungiyar suka ziyarci Jihar Legas.
Ya ce, “Ba mu shiga wani rudani ba, shugabancinmu daya, asalin wadanda suka kafa kungiyar Izala suna da wani sharadi da suka tsaya a kai, Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce musulmi suna kan sharadinsu, abin da suka yi yarjejeniyar za su tafi a kai, to suna kai sai dai in wannan sharadin zai halatta haram. Allah Madaukaki Yana cewa cikin surar Ma’ida, ‘Ku cika alkawuran da kuka yi a tsakaninku’. To ka ga ashe idan kungiyar ta shiga cikin rudani, babu shakka an bar abin da aka kafa ta a kai”.
Ya ce, ‘Ni abin da na fahimta, rudanin shi ne batun shugabanci inda ake cewa ‘Tsakanin shugaban majalisar malamai da shugaban kungiya waye shugaba?’ Masu fadar haka sun manta yadda dokokin kungiyar Izala yake. Tun farko, wadanda suka kafa ta sun tsara cewa shugaba na koli shi ne shugaban kungiya, wanda a karkashinsa akwai kwamitoci, wanda a cikinsu akwai kwamitin masu wa’azi. A kundin tsarin kungiyar Izala babu majalisar malamai. Na kalubalanci kowa, idan akwai wannan kalmar a cikin kundin tsarin dokokin Izala a nuna mini wurin. Duk lokacin da kwamitoci za su zartar da wani abu, doka ta ce dole sai sun tuntubi shugaban zartarwa, wanda shi ne shugaban kungiya”.
Ya kara da cewa lokacin da aka yi wa kungiyar rajista, shugabanta na farko shi ne Shaikh Maigandu, wanda rijistar kungiya take hannunsa kuma da ba shi ne shugaba na koli ba da ba a bar rajistar a hannunsa ba.
Ya bayyana cewa shugabanni da dama na kungiyar, kamar su Shaikh Isma’ila Idris da Shaikh Yusuf Sambo  ba su taba musanta cewa Shaikh Maigandu ba shi ne shugaba na sama ba.
Ya ce an sami sabanin ne lokacin da kungiyar ta hade daga bisani kuma aka sauke Shaikh Yusuf Sambo a matsayin mataimakin shugaban majalisar malamai aka nada Shaikh Jalo.
Albani ya goyi bayan wasu shugabannin kungiyar na reshen Jihar Legas da suke cewa bangarorin kungiyar Izala da suka hade kawance suke yi har yanzu.