✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabancin Majalisar Gwamnoni: Babu wanda ya isa ya dora wani a kanmu –Kwankwaso

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce babu wanda ya isa ya dora musu wanda zai shugabanci Majalisar Gwamnoni ta Najeriya domin sun…

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce babu wanda ya isa ya dora musu wanda zai shugabanci Majalisar Gwamnoni ta Najeriya domin sun san abin da suke bukata a siyasar kasar nan kuma a matsayinsu na ’yan Arewa wajibi ne a tuntube su kan abin da suke bukata ba a zaba musu wanda wani ke so ba.
Gwamna Kwankwaso ya bayyana haka ne a tattaunawa da manema labarai a Abuja, ya ce wasu mutane ne suka yanke shawarar kujerar shugaban Majalisar Gwamnoni ta Najeriya ta dawo Arewa ba tare da tuntubarsu ba. Ya ce, “Mu ’yan Arewa ne, kuma ina jin ya kamata a tuntube mu kana bin da muke bukata a Arewa. Wasu mutane sun yanke shawarar cewa mu karbi shugabancin Majalisar Gwamnonin Najeriya. Wannan ba zabinmu ba ne. Muna da zabinmu a zukatanmu. Mun san abin da muke bukata a harkokin siyasar kasar nan. Kuma koda muna bukatar haka, ba mu sa ran wani daban ya zaba mana, wajibi ne mu zaba da kanmu.”
Game da korafin da gwamnonin jihohin Bauchi da Benuwai Isa Yuguda da Gabriel Suswan suka yi cewa an ci amanar Arewa, Gwamna Kwankwaso ya ce tun kafin a gudanar da zaben ya gargadi Gwamnan Jihar Katsina Shehu Shema da Gwamnan Bauchi Isa Yuguda cewa ba zai goyi bayansu kan shugabanci majalisar ba.
“Na gaya wa Shema ‘kai makwabcina ne kuma dan uwana kuma dan uwanan, amma ba za ka zo ka ce min kana takararr a zabe ka ba, amma ka rika nuna kai dan takara ne kuma kana nuna kamar an aiko ka gare mu ne ba.’ Na fadi cewa ba zan zabe shi ba, kuma ba zan nemi wani ya zabe shi ba. Kuma zan tabbatar ya fadi a zaben. Na gaya masa haka ido da ido. Kuma a lokacin da nake gaya masa Sule Lamido yana wurin yana goyon bayana, gwamnonin Adamawa da Neja suna wurin. Wannan ya sanya wasu mutane suka ce Shema bai samu goyon bayan Arewa ba. Isa Yuguda kuma ya zo gare ni, na gaya masa cewa har yanzu ni dan kauye ne, kuma ina yin abubuwana kamar bakauye. A kauyena Kwankwaso da ke Kano, idan dan takarar kansila ya zo wurin dattawa da safe cewa yana son tsayawa takarar kansila kuma suka amince masa, to idan wani ya zo da rana ya nemi su goya masa baya, mutanen kauyen za su gaya masa ya makara. Ba mu son Shema ne saboda muna son mu zabi shugabanmu da kanmu. Yanzu kai ma ka zo ta irin wancan hanya. Da ya nace, kuma ganin a gidana yake, ban so in tsananta masa kamar yadda na yi wa Shema ba.”
Game da yadda batun amincewa da Gwamna Jang a matsayin dan takarar Arewa, Gwamna Kwankwaso ya ce, shi ya ba da sunan Jang don zabensa kan wannan mukamin duk da cewa yana goyon bayan takarar Amaechi, saboda rukunin gwamnoni 16 “G16” sun rude suna son tsayar da dan takarar da zai kalubalanci Amaechi.
 “Ni na ba su sunan Jang kuma na nemi Gwamnan Benuwai ya goya min baya. Na lura sun yi matukar rudewa, kuma koda bayan zaben ba za su amince da nasarar Amaechi ba. Sai muka ba su wanda muke jin zai jagoranci bangaren marasa rinjaye. Kuma lokacin da muka bar wurin sai suka yi ganawarsu suka amince da shi. A karshe sun gabatar da shi gaban babban taron Majalisar Gwamnonin.  A wurin wannan taro mun shaida musu muna so Amaechi ya ci gaba da zama shugaban majalisar. Mun gudanar da zabe saboda an kasa samun daidaito,” inji shi.
Daga nan sai ya gargadi gwamnonin biyu na Bauchi da Benuwai da suka fice daga Majalisar Gwamnonin Arewa kan zargin cin amana daga takwarorinsu, inda ya ce sun yi babban kuskure a fagen siyasarsu, kuma zai yi wuya nan gaba su sake cin wani zabe a Arewa.
“Matsalar da ke cikin abin da suke fadi, ita ce ba sa tare da mu (gwamnonin Arewa). Abin da muke cewa (Majalisar Gwamnonin Najeriya) ba ruwanta da siyasar Majalisar Gwamnonin Arewa, inda muke da kadarori da basussuka. Ko a mulkin soja ko na farar gwamnonin na halartar tarurrukanta saboda wajibi ne ka je ka bayyana al’amuran da suka shafi al’ummarka a can.”
Ya kara da cewa, “A yanzu idan ka fice daga Majalisar Gwamnonin Arewa, lokacin da gwamnonin jihohin Yamma ke taro ba yadda za a yi ka shiga cikinsu. Ina mamakin inda za su je. Ina son gaya muku idan suka ci gaba da haka, ban ga yadda za a yi su ko wadanda za su tsayar takara su ci zabe a Arewa ba. Ina jin zai fi kyau su fara tsayar da ’yan takararsu a zabe daga wajen yankin Arewa. Ba su san suna yi mummunan kuskure ba. Me Arewa ta yi musu? Wa ya gaya musu Arewa ba ta goyon bayan Amaechi? Idan za ka dauki mataki kada ka dauke shi a lokacin da kake cikin fushi. Kada ka ce saboda kana son ka burge wani domin a dauke ka gwamna nagari, za ka mance gidanka, ka yi watsi da jama’arka, kana cin zarafinsu…. Wannan babban kuskure ne. Ba zan taba kuskuren fitar da Kano daga Arewa ba. Masu irin wadannan kalamai suna tafka kuskure. Zai yi kyau su dawo cikin hayyacinsu domin amfanin kansu.”
Kwankwaso ya nanata muhimmancin da Majalisar Gwamnonin Arewa ke da shi, inda ya ce a Majalisar Gwamnonin Najeriya abin da gwamnoni ke yi shi ne bita kawai, amma a Majalisar Gwamnonin Arewa ana tattaunawa tare da daddale batutuwa sosai. “Jama’a suna matukar kishin Majalisar Gwamnonin Arewa, kuma a duk lokacin da ka cire kanka, jama’a za su iya yin shiru su nuna maka karshenka a lokacin da ya dace,” inji shi.