✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabanni su ji tsoron Allah —Shaikh Dahiru Bauchi

Shehin malamain ya kirayi shugabanni su yi adalci malamai kuma su yi kira ga zaman lafiya

Mashahurin malamin Musulunci, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya kirayi ga shugabannin siyasa da na addini a Najeriya su ji tsoron Allah su yi wa mabiyansu adalci ba tare da nuna bambanci ba.

Shehin malamain ya yi kiran ne a taron kaddamar da littafi da bidiyon tarihinsa mai taken ‘Lisanul Faidha (Voice of Islam)’, wanda kungiyar Arewa Next Step for Tinubu (ANEST) da kuma Blue Bells Promoters suka gudanar a Abuja.

“Allah Ya umarci shugabanci tun daga matakin iyali, hakimai, shugabannin kananan hukumomi zuwa shugaban kasa da su tsare gaskiya, su yi wa mabiyansu adalci su kuma tababtar da aminci”, inji shi.

Shugaban na Darikar Tijjaniya a Najeriya ya kuma yi kira ga malaman addini da su yawaita yin kira ga zaman lafiya da rungumar juna tsakanin mabiya.

Ya kuma yi kira ga matasa da su nemi ilimi wanda shi ne kashin bayan gudunmuwar da za su iya bayarwa wajen cigaban kawunansu da kuma al’umma.

Shi ma da yake jawabi a wurin taron, Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari ya yi kira ga matasa da su yi koyi da kyawawan dabi’un shehin malamin musamman na sadaukar da kai wurin hidimta wa Musulmi.

Masari ta bakin hadiminsa kan Ilimin Gaba Sakandare, Muhammad Bashir ya bayyana shehin a matsayin kogin ilimin Al-Kur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW).

Shugaban Cibiyar Nazarin Tsaro da Adana Bayanai (CDSD) a Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji (NDA), Farfesa Usmna Tar, a nasa jawabin ya yi kira ga shugabanni da su kasance masu jin tsoron Allah a koyaushe, su kuma guji shagaltuwa da abin duniya da bin son zuciya.

A jawabinsa kan sarkakiyar kalubalen da ke cikin shugabanci, Farfesa Usman Tar ya shawarci shugabanni da su kiyaye rikon amana, gaskiya, da tausayin jama’a musamman masu rauni.

Shi ma Darakta-Janar na ANEST, Malam Musa Usman, ya ce kungiyar ta mayar da hankali “wajen kaddamar da tarihin Shaikh Dahiru Bauchi ne saboda tsohon Gwamnan Jihar Legas, Ahmed Bola Tinubu, wanda shi ne ya ba su karfin gwiwar kafa kungiyar na tarayya da shehin malamin ta fusktar ba da jagoranci da kuma taimakon al’umma”.