✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin APC sun shiga tsakanin majalisa da Gwamnan Gombe

Rikicin da ya kunno kai a Majalisar Dokokin Jihar Gombe wanda ya kai ga tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Alhaji Shu’aibu Adamu Haruna, daga Kwami ta…

Rikicin da ya kunno kai a Majalisar Dokokin Jihar Gombe wanda ya kai ga tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Alhaji Shu’aibu Adamu Haruna, daga Kwami ta Gabas, ya sa masu ruwa-da-tsaki a Jam’iyyar APC da kusoshin bangaren Gwamna sun shiga tsakani.

An fara kai ruwa rana ne a tsakanin Gwamnan da ’yan majalisa kan           kin samar musu da motocin hawa bayan rantsar da su, amma sai ga shi ana shirin bai wa sababbin kwamishinonin da aka rantsar motocin, wanda haka ya sa suka daina halartar duk wani taro na gwamnati. ’Yan majjalisar sun zargi tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar da halartar wani taro na gwamnati da kuma alakarsa da Gwamna.

Ganin zaman doya da manja tsakanin bangaren Gwamnan da ’yan majalisar na kara ruruwa ne masu ruwa-da-tsaki na Jam’iyyar APC suka yi zama na musamman da ’yan majalisar don shawo kan matsalar.

Bayan kammala zaman dan majalisa mai wakiltar Yamaltu ta Gabas Adamu Sale Pata, wanda shi ne ya gabatar da kudirin tsige tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar, ya bayyana wa manema labarai cewa yanzu sun sasanta ba su da wata matsala da Gwamna.

“Canjin da muka yi ba mu gamsu da tafiyar da shugabancin tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar ba ne shi ya sa muka canja shi,” inji Pata.

Adamu Sale Pata, ya kara da cewa “Sashi na 92 karkashin kashi na 2 na kundin tsarin mulkin kasa ya ba mu dama tun daga kan Shugaban Majalisa har Mataimakinsa da duk wani mai rike da mukami a majalisa idan ba mu gamsu da shi ba, mu canja shi kuma wannan canji da muka yi bai saba wa dokokin majalisa ba.” Sai dai tambayar da wakilinmu ya yi mas cewa me ya sa ba a gansu a wajen rantsar da sababbin kwamishinoni da kaddamar da motocin Gombe Line ba, ya kasa bada amsa duk da ya ce ba su da wata matsala da Gwamna.

Taron ya samu halartar dukkan ’yan majalisar jihar 24 da tsohon Mataimakin Gwamna Sanata Joshu’a Lidani da tsohon Ministan Sufuri Abdullahi Idris Umar da Alhaji Habu Mu’azu da Sanatan  Gombe ta Arewa Sa’idu Ahmed Alkali da Alhaji Yunusa Yakubu da sauransu.