Aminiya

Shugabannin Hausawan Ibadan sun bukaci jama’arsu su girmama doka

Sarkin Hausawan Mobil Ring Road a Ibadan Alhaji Sule Garba ya ja kunnen jama’arsa mafi yawancinsu kananan ’yan kasuwa da ’yan acaba da leburori cewa su tabbatar cewa, suna girmama dokokin da mahukunta suka shimfida a kan hanyoyi da kyautata zamantakewa tsakaninsu da jama’ar gari. Ya ce, “Mun nada muku amintaccen shugaba da mataimakansa da za su rika lura da al’amuranku ta fannin shiga tsakaninku da jami’an tsaro, mu kuma za mu yi kokarin ganin sun gudanar da ayyukansu tsakani da Allah domin zama lafiya da kwanciyar hankali.”

Sarkin Hausawan ya bayyana haka ne a wajen taron da ya gudanar da jama’arsa a fadarsa da ke Unguwar Mobil a Ibadan, ya ce “Yau fiye da shekara 30 muke zaune a wannan gari na Ibadan ba mu taba samun  matsala a tsakaninmu da jama’ar gari ba. Saboda haka nake jan kunnenku kada ku kuskura ku bata mana wannan kyakkyawar zamantakewa,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Shi kuwa Wakilin Sarkin Hausawa Malam Ibrahim Nasale, ya fara godiya ga Allah ne game da irin shugabancin da suke yi, inda ya ce, “Zaman lafiya da muka samu tunda muka fara shugabanci a wannan unguwa ta Mobil shi ne babban ci gaban da muke godiya ga Allah (SWT) da kuma jinjina wa mahukumtan Jihar Oyo da sarakunan gari da suke sauraren koke-kokenmu tare da share mana hawaye gwargwado a kowane lokaci. Muna zaune da iyalanmu a cakude da Yarbawa muna gudanar da kasuwanci lafiya babu wata tsangwama ko lakutar hancin juna. Saboda haka muke  kira ga mutanenmu musamman ’yan acaba su guje wa shiga cikin bata-gari masu amfani da baburansu wajen aikata miyagun ayyuka.” Ya kara da cewa: “Ina tabbatar muku duk wanda ya jefa kansa cikin mugun hali, za mu kama shi mu mika wa jami’an tsaro domin hukunta shi. Ba za mu amince da zama da miyagun mutane ba a wannan lokaci na tabarbarewar tsaro.”

Da yake tofa albarkar bakinsa Babban Limamin Masallacin Mobil Ustaz Is’hak Garba, ya yi addu’o’in Allah Ya samar da zama lafiya mai dorewa a birnin Ibadan da Jihar Oyo da kasa baki daya.

ADVERTISEMENT

Sai dai ya ce, “Ya kamata mu ma mu bayar da gudunmawarmu ga sabon tsarin tsaron kasa da mahukunta suka bullo da shi ta fannin bayar da labarin miyagun ayyuka ga shugabanninmu da ofisoshin jami’an tsaro wanda hakan zai taimaka wajen cimma burin mahukunta a kan tsaron kasa.”