✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin Kungiyar ’Yan jarida sun saba laya a Katsina

An rantsar da sababbin shugabannin Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Katsina  a wani biki da aka yi a hedkwatar kungiyar da ke …

An rantsar da sababbin shugabannin Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Katsina  a wani biki da aka yi a hedkwatar kungiyar da ke  garin Katsina bayan da shida daga cikinsu  suka ci zabe babu hamayya.

Kujera daya da aka fafata zabe a kanta ita ce ta Ma’aji wacce aka kara a tsakanin Umar Isyaku Ogunse daga Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar da Bishir Labaran Albaba daga Gidan Rediyon Jihar, inda Bishir Labaran ya samu nasara.

Aminiya ta tuntubi sabon Shugaban Kungiyar, Alhaji Tukur Hassan Dan-Ali, kan abin da yake shirin yi wa kungiyar. Sai ya ce yana da abubuwa uku da yake shirin aiwatarwa lokacin mulkinsa da suka hada da kyautata da’a ta hanyar tabbatar da cewa kowa ya san aikinsa da abin da ya kamata ya yi, tare da kokarin rage bazuwar tsegunguma a tsakanin ’ya’yan kungiyar. Sannan akwai batun sake farfado da horo da horarwa ga ’yan jaridar da ke aiki a jihar ta hanyar neman masana a kan aikin tare da hada kwiwa da gwamnati da makarantu da sauran masu ruwa-da-tsaki a harkar aikin jarida domin tafiyar da aikin a zamance da kara wa ’yan jaridar zimma a aikinsu.

Ya ce zai kara zaburar da hanyoyin samun kudaden shiga ga kungiyar ta hanyar inganta Sakatariyar Kungiyar da  karin gine-gine da za su samar da kudin shiga tare da wadanda ’yan kungiyar za su yi amfani da su musamman a lokacin da suke bukatar wajen hutawa bayan dawowa daga aiki ko yin nazari ko zama don rubuta labari.

Alhaji Tukur ya ce, zai kara kulla alaka da sauran kafofin  labarai da ke jihar har da na waje domin ganin cewa ’yan jaridar da ke aiki a jihar sun zama abin koyi ga saura.

Wadanda aka rantsar sun hada da Tukur Dan-Ali a matsayin Shugaba da Abdullatif Yusuf, Mataimakin Shugaba, sai Aliyu Yunusa Kofar Soro, Babban Sakatare da Sama’ila Adamu, Mataimakin Sakatare. Kujerar Sakataren Kudi ta tafi ga Rabi’u Ibrahim, sai Ma’aji Bishir Labaran Albaba, yayin da Inusa Umar Faruk ya zamo Mai Binciken Kudi na Kungiyar, kuma za su jagoranci kungiyar ce na tsawon shekara uku.

’Ya’yan kungiyar sun kai ziyarar ban girma ga Gwamna Aminu Masari bayan an rantsar da su, inda Gwamnan ya yaba yadda suka aiwatar da zaben cikin lumana, sannan ya ja hankalinsu kan su ji tsoron Allah a lokacin da suke jagoranci da kuma aiwatar da ayyukansu. Su kuma tabbatar suna bayar da sahihan labarai ga al’umma ta hanyar bayyanar da gaskiyar abin da ya faru kasancewar na tsakiya a bangarori biyu cikin al’umma.