✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin PDP na Sakkwato sun yi farin ciki da komawar Wamakko Jam’iyyar APC

Shugabannin Jam’iyyar PDP na Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin shugabanta na farko Alhaji Arzika Tambuwal ne suka yi gangamin nuna farin ciki da Gwamnan Jihar…

Shugabannin Jam’iyyar PDP na Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin shugabanta na farko Alhaji Arzika Tambuwal ne suka yi gangamin nuna farin ciki da Gwamnan Jihar Alhaji Aliyu Wamakko ya fice daga jam’iyyar da kuma nuna goyon bayansu ga shugabanta na kasa Alhaji Bamanga Tukur da kuma Shugaba Jonathan.
Shugabannin wadanda suka gudanar da taro a ranar Lahadin da ta gabata a otel din dankani da ke Sakkwato, shugaban taro Alhaji Arzika Tambuwal ya ce “A matsayinmu na halattatun ’yan Jam’iyyar PDP muna kara jaddada goyon bayanmu ga shugabanninmu na kasa karkashin jagorancin Bamanga Tukur da Shugaba Jonathan. Kuma muna son gayawa jama’armu siyasar wannan jiha ta samu ci gaba ta dalilin komawar Gwamna Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko Jam’iyyar APC, bayan dukkanmu mun san jam’iyyun da suka narke suka samar da APC sun yi ta nuna gazawarsu a zabubbukan da suka gabata inda jam’iyyarmu ta PDP ke rinjaye saboda kyakkyawan shirin da take da shi.”
Shugaban ya ce daga yanzu sun fara aiki tukuru domin ganin sun dawo da martarbar jam’iyyar don cin zabe a shekarar 2015, “domin tun a 1999 ne muke yi wa jam’iyyarmu aiki ba tare da nuna gazawa ba, ba don da mu aka kafa jam’iyyar ba ko don na rike mukamin minista a gwamnatin PDP ba, sai don kyawawan manufofinta,” inji shi.
Tsohon shugaban PDP na shiyyar kudancin jihar Alhaji Magajin Kojiyo ya ce “Muna nan cikin PDP daram annoba ta fita cikinmu, shekara takwas aka yi ana cin amanarmu, to ga shi yanzu mun fara ganin sakayya.”
Ya kara da cewa “karya ce wani ya gaya mana wai ba mu iya cin zabe domin koda Wamakko ya zo muna da ciyamomin kananan hukumomi 16 da kansiloli sama da 200, yanzu muna cikin farin ciki, za mu tafi Abuja mu karbo jam’iyyar a fara aiki.”
Taron ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar kamar Sanata Abubakar Gada da Abdallah Wali da Abdullahi Kiriyo Yabo da Aliyu FC da Sanata Ilah Gada da tsohuwar shugabar mata Hajiya Rabi ’Yar Kangiwa da Mahe Dange da Abdullahi Shuni yayin da tsohon minista Yusuf Suleiman ya aiko da uzurin cewa ba ya kasar nan.