✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin PDP na yanke hukunci ne cikin maye – Sale Taki

Shugaban karamar Hukumar Kazaure a Jihar Jigawa kuma daya daga cikin masu fafutikar ganin Gwamnan Jihar, Alhaji Sule Lamido, ya fito takara a zaben Shugaban…

Shugaban karamar Hukumar Kazaure a Jihar Jigawa kuma daya daga cikin masu fafutikar ganin Gwamnan Jihar, Alhaji Sule Lamido, ya fito takara a zaben Shugaban kasa a shekara ta 2015. Alhaji Sale Yahaya Taki ya ce, matsalar Jam’iyyar PDP ita ce rashin shugabanci nagari wanda hakan ne ya sa a lokacin da zabe ke gabatowa ake korar wasu jiga-jigai daga jam’iyyar.
Alhaji Sale Taki ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce, “Matsalar shugabannin jam’iyyarmu ta PDP ba sa daukar matakin da ya dace domin gyara, suna yanke hukunci ne a lokacin da suke tsakiyar mayen giya, watakila suna amfani da kwayoyin sa maye ne shi ya sa ba sa gane kura-kurensu.”
Alhaji Sale Taki ya ce a duk fadin kasar nan babu wanda ya cancanci ya tsaya takarar shugabancin kasar nan ban da Gwamna Lamido saboda irin gwagwarmayar da ya sha a baya, kuma ga shi mutum marar tsoro da jajircewa da tsayin daka wajen ganin ya kwato wa talakawa ’yanci.
Shugaban ya ce ko Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan dole ya mara wa Gwamna Lamido baya idan ya fito takara a shekarar 2015 saboda irin gudunmawar da ya ba shi a baya, “sanin kowa ne babu irin maganganun batanci da ba a gaya wa Gwamna Lamido ba a kan jajircewarsa wajen ganin Jonathan ya zama Shugaban kasa, don haka muna da tabbacin Jonathan dattijo ne ba zai yi wa Lamido bi-ta-da-kulli ba,” inji shi.
Ya ce a gwamnonin kasar nan Lamido ne yake amfani da kudin da yake amsa daga Tarayya wajen samar da ayyukan raya kasa domin al’ummar jiharsa, inda ya ce kowa ya shiga Jihar Jigawa ya san an samu canji sabanin yadda Gwamna Saminu ya bar ta a wulakance, ma’aikatu a wargaje babu gidajen ma’aikata babu ruwa babu wutar lantarki kuma matasa na ta gararamba a titunan jihar.
Sai ya ba ’yan Najeriya tabbacin tsaron lafiyarsu da dukiyarsu muddin suka zabi Gwamna Lamido a shekarar 2015. Ya ce halin rashin zaman lafiya da kasar nan take fuskanta Jigawa ta zama zakarar gwaji wajen zaman lafiya.
Ya ce Jam’iyyar PDP jam’iyya ce da ke da mutunci a fadin Afirka kuma tana da mutane masu kima da gogaggun ’yan siyasa, amma matsalarta ba ta da shugabanni na kwarai. “Na rasa abin da yake damunsu ko kwaya suke sha ko kuma suna shan burkutu ne kafin su yanke hukunci, ga zabe yana zuwa amma sai ka ji an ce wai jam’iyyar za ta kori wancan Gwamna daga cikinta ko ta kori wancan, hakan ba ya da nasaba da hankali domin aiki ne na marasa hankali,” inji shi.