✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin ’yan Arewa mazauna Benin sun yi taron gyaran rayuwa

Shugabannin bangarorin ’yan asalin Arewa mazauna garin Benin sun gudanar da wani taro na musamman a karkashin jagorancin shugaban al’ummar Arewa, Alhaji Badamasi Saleh, inda…

Shugaban al’ummar Arewa, Alhaji Badamasi Saleh    Shugabannin bangarorin ’yan asalin Arewa mazauna garin Benin sun gudanar da wani taro na musamman a karkashin jagorancin shugaban al’ummar Arewa, Alhaji Badamasi Saleh, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka danganci harkokin rayuwarsu.
Daga cikin batutuwan akwai lamarin samar da hanyoyin ci gaba da hadin kai da zaman lafiya tsakaninsu da sauran jama’ar jihar, kamar yadda jagoran taron ya shaida wa Aminiya, bayan kammala taron a ofishinsa.
Ya ce, “Mun yi wasu tsare-tsare ta yadda za mu samu saukin wayar wa al’umma kai kan al’amuran da suka shafi ci gaba da kuma yadda za a sami dorewar kyakkyawar zamantakewa tsakanin jama’a. Don cimma wannan buri ne ma ya sa muka yanke cewa daga yanzu shugabannin bangarorin da malaman addini za su zage dantse kan wayar wa jama’a kai kan muhimman abubuwa da suka hada da zaman lafiya da bin doka da oda. Wannan hanya ita ce muke sa ran za ta taimaka wajen kara maida wa mutanenmu ’yan Arewa daraja a wannan jihar, har da kasa baki daya”.
A karshe shugaban ya nuna cewa ba za a iya cimma wannan buri ba matukar ba a sami hadin kai da goyon baya daga jama’a ba.  Sannan ya bayyana cewa ta haka za a samar da wakilci na adalci wajen saduwa da mahunta a duk lokacin da bukatar haka ta taso.
Haka nan taron ya zartar da cewa za a ci gaba da tuntubar juna tare da gudanar da taron akalla sau daya cikin kowane wata domin tattaunawa a kan matsalolin da ka taso cikin al’umma da nufin magance su.