Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Shugabar Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ta ziyarci Najeriya

Shugabar Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya UN GA María Fernanda Espinosa Garcés za ta ziyarci fadar shugaban Najeriya Abuja a yau Talata don ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.

Wakilinmu ya bayyana cewa, Shugabar ta isa fadar shugaban kasar da misalin karfe 11:40 na safe. Ana saran Ministoci da manyan jami’an gwamnatin Najeriya za su halarci ganawar da za a yi tare da shugaba Buhari.

ADVERTISEMENT