Shugba Buhari ya ba Amokachi Ambasadan Kwallon Kafa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin tsohon dan wasan kwallon kafan Najeriya, Daniel Amokachi a matsayin Ambasadan Kwallon Kafan Najeriya.

Amokachi ya kasance cikin ’yan wasan da suka ciyo wa Najeriya Gasar Cin Kofin Afirka a shekarar 1994, da Gasar Olympic na Atalanta a shekarar 1996.

Haka kuma, Daniel Amokachi ya samu nasara lashe Gasar Kalubale wato FA Cup na Ingila da kulob din Everton a shekarar 1995.

Bayan ya yi ritaya daga wasanni, ya zama kwararren koci, inda ya horar da kungiyoyi irin su Nasarawa United da Enyimba da kuma Mataimakin Koci na Super Eagles.

A matsayinsa na ambasada, zai taimaka wa Ministan Wasanni wajen nemo ’yan wasa da kuma cigaban wasanni a Najeriya.

ADVERTISEMENT
Share