Da Dumi Dumi

Siasia ya nemi taimako, bayan mahaifiyarsa ta shafe kwana 70 a hannun masu garkuwa

Tsohon Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa Samson Siasia ya nemi Gwamnatin Tarayya ta taimake shi wajen kokarin da yake yi na kubutar da mahaifiyarsa daga hannun masu garkuwa da mutane da a yanzu take hannunsu.

An sace Misis Ogere Beuty Siasia, mai shekara 79 tun ranar 15 ga watan Yuli bana a gidanta da ke Odini, a Karamar Hukumar Sagbama a Jihar Bayelsa.  Duk wani kokari da aka yi don ganin an kubutar da ita da kuma wata mai shekara 66 mai suna Florence Donana da  jikarta  zuwa yanzu ya ci tura.

A farkon watan Satumbar ne Siasia ya bayyana ma manema labarai cewa duk da yake masu garkuwa da ita sun karbi kundin fansa Naira miliyan daya da rabi har zuwa lokacin ba su sako masa mahaifiyarsa ba. Ya ci gaba da cewa masu garkuwa da mutanen maimakon haka sai suka sako surukarsa kuma a lokaci guda suka kama wanda ya kai musu kudin fansar.

Mai horar da ’yan wasan wanda shi kansa yake kokarin wanke kansa game da dakatarwar da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta yi masa dangane da zargin karbar rashawa, ya ziyarci Ministan Wasanni Sunday Dare a kwanakin baya inda ya bukaci taimakon gwamnati. An ruwaito cewa Siasia yana da yakinin cewa Gwamnatin Tarayya ce kawai za ta iya kawo masa dauki don ganin an kubutar da mahaifiyar tasa daga hannun masu garkuwa da ita.

Duk da yake ’yan Sanda a Jihar Bayelsa sun tabbatar da cewa suna kokarin kubutar da ita ba tare da wani abu ya faru da ita ba, tsohon dan wasan gaba na kungiyoyin kwallon kafa na Nantes da Lokeren ya bayyana cewa karfinsa ya kare kuma yana cikin wani hali da yake neman taimakon kasarsa da ya yi wa aiki a lokacin kuruciyarsa.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya