Search
Subscribe
Siddabarun sihirin sirrin sarari (1)

Siddabarun sihirin sirrin sarari (1)

Karatun kariya,

Kankane kame-kamen karbe kaya

Ko kuwwar kukan kuliya,

Kauce-kaucen karafkiya,

Karon-battar kulle kurciya.

 

Zarar zantukan zuzuta zazu,

Gumurzun gudun gunzu,

Digirgiren daukar Dan Buzu,

Dawainiyar dazu-dazu,

Kiren karairayin karar Karkuzu.

 

Amincin amanar aminai,

Kundin bayanai,

Kare rayuka,

Zaman zauren zaurancen zantuka

Aikin alkinta awalajar aninai.

 

Mutane masu muhimmanci,

Al’umma akai wa azanci,

Baje batutuwan butulci,

Bangarancin batagarin batanci,

Carin ce-ce-ku-cen caccakar ci-ci.

 

Sihiri.

Siddabarun sirri,

Sa-in-sar sarari,

Sukurkucewar sufuri,

Salon sunce sasari.

 

Kalallame kalaman kurtu,

Kutunguilar kutu-kutu,

Karime-karimen kudi,

Kurda-kurdar kurdi,

Hayayagagar hana hutun huntu.

 

Tantagaryar tafiyar tsutsar talifi,

Tarin tallafi,

Taga-tagar tafkeken tafi,

Tattagar tattare tufafi,

Tabaryar turamen tasarrufi.

 

Garkame gambun gararuma,

Tsimin tsamiyar tsamin tsantsama,

Kulle kurciyar kai-kawon kunama

Lallashin lalamar lamma-lamma,

Gungunin guna-gunin gulma.

 

Manyan kwabo,

An hana ku kwambo,

Balle bokokon bobo,

Sai sauya salo sabo,

An dai yi kabo-da-adabo.

 

Garkuwa,

Gagara-kuwwa,

Tsautsayin tsiyatakun tsuwwa,

Wariyar  ’ya’yan Bora da Mowa,

Haurobiyawa.

 

Gingimemiyar guduma,

gande-ganden gardama,

Gogoriyon gabotarin girma,

Gagarar garnakakin gunduma,

Gambun garkama.

 

Takun tattaunawar takaddama,

Tabarar  tumbin tumun tuma,

Tinkahon torokon takama,

Tarairayar tereren tantama,

Takarlar  taho-mu-gama.

 

Sasarin sunkurun sirri,

sarke-sarken sare-sarin sari,

Shammatar shirin sharri,

Sunce sasari siriri,

Sarkakiyar sunkutar samari.

 

Zaratan zagayen zaki,

Alamta alayen alkinta alkaki,

Muku-mukun make-maken mamaki,

Marairacewar mai masaki,

Muzuran murkushe musaki,

 

Zakakuran zarge-zargen zargi,

Aringizon antayo ashariya shirgi-shirgi,

Zakalkalewar zugar zuga-zugi,

Gwagwagwar gwaramar gwara kan agwagi,

Hatsaniyar hargowar hargagi.

 

Juwa-juwar juyin jaki,

Doke-doken daga daki-daki,

Koke-koken kukan kakaro kaki,

Bambamin bankaurar baki,

Raurawar razanar raki.

 

Dama-damar dundumin duma,

Gagarar gadarar gardama,

Kumbiya-kumbiyar karma-karma

Kame-kamen kyankyamin kyama

Janjanin jaye-jayen jimamin jima.

 

Gwaramar gararambar gambarar gigi,

Mamungar musun magagi,

Zabarin zaburar zogi,

Rodi-rodin ragargazar rugugi,

Kululun kumajin kugi.

 

Makamar motsa muka-mukin miki,

Gararumar gyara girki,

Gwagwagwar gwaramar gwanki,

Mutum mai mulki,

Kaka-gidan kariyar kulki.

 

Manyan mutane,

An ba ku kariya kane-kane,

An bi ku an kankane,

An zo ganne na-mujiya an manne,

Garkuwar garkame wane da wane.

 

Kariyar kebabbu,

Zagaye zababbu,

Tunzurar  tababbu,

Kwadon kwakin kwababbu,

Rugumniyar ragargazar rubabbu.

 

Kwabe-kwaben kwadon kwaki,

Subul da bakan sakin baki,

An yasar da aura ana jibgar taiki,

Mummunar yabanya ta sha taki,

Aika-aikar assasa asarar aiki.

 

Mai hali,

A ke kwantarwa da hankali,

Talalar talaucin talaka tai tarin tattali,

An yi masa ginin ganuwar tubali,

Ana jin jikin balbalin bala’in balli.

 

Wallafa wagegen littafi,

Na kare manya daga masu laifi,

Talaka an bar shi da dafi,

Yana fama da masu kulumboton tsafi,

An hana dibar ruwan rafi.

 

Alhali an san suna nan,

Masu zaman dirshan,

Su aikata wancan,

Su damalmala wannan,

An ki a bi su nan-nan.

 

Ana  ta bin bahasi,

Mai jefa wasi-wasi,

Ko a samu tara taro da sisi,

An samu izinin lasisi,

Talalar talaucin talaka ba asi.

 

An hana biyan fansa,

An bi komai an farfarsa,

Wai dan halak ka fasa,

Miyagu sun samu fursa,

Ana ta dasa dasisa.

 

Inganta ingarman iyalai,

Lallai-lallai,

Dumuiniyar daddale dalilai,

Rayuka ai musu dillancin dillalai,

Walkiyar wala-walar makale makullai.

 

A bai wa kowa kariya,

Rayuka da dukiya,

A yasar da wariya,

Talaka na fama da taraliya,

Kun tunzuro turjiya.

 

A Haurobiya,

Ana gani da na-mujiya,

Kun hana tuka tuwo da muciya,

Sanwarku na zababaka a tukunya,

Kundumbalar kunduge koshin koshiya.

 

Ai himma,

Kowa yai kama-kama,

A daina dama-dama,

A bi komai da lalama,

Sai kasa ta san makama.

 

Masu fuka-fukin tashi,

Tashintashina ta tashi,

Ta turaro tasshi,

Ruruwar wutar garwashi,

Zafin kuna na ta gashi.

 

Kyawawan ta’adu ai musu harsashi,

A koyar da kwabin siminti da yashi,

Ai gingimemen ginin tsawon tsinin mashi,

Samarin-kusu sai sun kwashi kashi,

A watsar da wukaken wa-ka-ci-ka-tashi.

 

Mu zo mui aiki mu zanki nishi,

Mui tattaki ba dingishi,

Tulluwar tumbi tai nunin koshi,

Tuwo da miyar tauna tantakwashi,

Ai albashi ba bashi.

 

Ku zo ai adashi,

A samu abin girka dashishi,

Amare su zam kunshi,

Gidaddaji baibaye da kanshi,

Rayuwar magidanta tai ta armashi.

 

Kasa ta zam ba kaskanci,

Ko wautar wargin wulakanci,

A dai cire sasarin kunci,

A daina jikkatar jakkanci,

Jibgin  jibar keta ’yanci.

 

Shagwabar sheke-ayar shawagi,

Wautar walagigi,

Watangaririyar wargi,

Wulkice-wulkicen wurgi,

Hantare-hantaren hatsaniyar hargagi.

 

Tsiwar tsurkun kiyasin kirgaggu,

Miyagu masu kulla tuggu,

Sai mun kama musu kugu,

A tamke shirga-shirgan shaggu,

A garkame su a lungu.

 

Muhimman mazauna muhalli,

Tattaunawar taron tattali,

Tsamin tsama tsilli-tsilli,

Dundumin damuwar danne dalili,

Zamiyar zogin zullumin zilli.

 

Mu natsu mu daina magagi,

Ko giringidimin gigi,

Ko jefa azargagiyar zargi,

Wasu sun bi zugar Zagi,

A daina dura ashariyar zagi.

 

Malami da dalibi,

Ba ruwanku da kinbibi,

Ko tsokale-tsokalen hatsabibi,

Zantuka zaro-zaro tsibi-tsibi,

A bi komai bi-da-bi.

 

A dai yi kyakkyawan dubi,

Duban dubarudun madubi,

Kowa ya bibiyi littafi babi-babi,

Limbu-limbun lambuna labi-labi,

Ziryar zaburar zabbi.

 

Kar a kama wa mutum kuibi,

Ya ji zogin zazzabi,

Ko kurungu ya samu tabi,

Gagantsarar gabobi,

A zo ba a da zabi.

 

Ai wa kowa alfarma,

Har a samu makama,

A samu saukin fama,

Sai mu bazama,

Ba sauran zama.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin