✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siffofi 20 na mace tagari

Samun nagartaccen gida abu ne mai matukar muhimmanci a zamantakewar iyali. Shi kuwa gida ba ya zama nagartacce sai da mace tagari, wadda take tattare…

Samun nagartaccen gida abu ne mai matukar muhimmanci a zamantakewar iyali. Shi kuwa gida ba ya zama nagartacce sai da mace tagari, wadda take tattare da siffofi ababen koyi da za su taimaka mata wajen tafiyar da gidan yadda ya kamata. Don haka ga wasu daga cikin siffofin da suka kamata mu yi nazari a kansu don gane wace ce mace tagari?  Siffofin sun hada da:

  1. Ta kasance mai riko da addini, ba mai sakaci da shi ba.
  2. Ta kasance mai gaskiya da rikon amana a koyaushe.
  3. Ta sanya Allah a ranta a duk al’amuranta na yau da kullum.
  4. Ta zama mai shigar mutunci, misali sanya hijabin da zai rufe mata jikinta yayin da ta fita zuwa unguwa.
  5. Ta kasance mai girmama iyaye da ’yan uwa da abokan mijinta.
  6. Ta kasance mai yawan kwalliya da ado ga mijinta.
  7. Ta kasance kwararriya wajen iya girki.
  8. Ta kasance mai godiya ga abin da mijinta ya kawo mata, kada ta raina abin da mijin ya kawo.
  9. Ta kasance mai gaggawar amsa kira yayin da maigida ya kira ta zuwa shimfidarsa.
  10. Ta kasance mai kiyaye dukiyarsa da duk wasu kayayyakin da yake amfani da su.
  11. Ta kasance mai rufa wa mijinta asiri, ba mai watsa sirrinsa ba.
  12. Ta kasance mai ba shi hakuri cikin lalama yayin da ta yi masa laifi.
  13. Ta kasance mai nuna farin ciki idan abin farin ciki ya same shi da nuna bakin ciki idan abin bakin ciki ya same shi.
  14. Kada ta yabi mijin wata alhali tana tare da mijinta.
  15. Ta kasance mai kwantar wa mijinta hankali yayin da yake cikin damuwa.
  16. Kada ta ba wata ko wani dama ya ji sirrinsu (ita da mijinta).
  17. Ta kasance mai kokarin neman ilimi da aiki da shi.
  18. Ta kasance mai nisantar abin da ba ya so, ta kuma rika kusantar abin da yake so.
  19. Ta kasance mai bin umarnin yi ko bari abin da yake so da wanda ba ya so, sannan ta nuna masa so da kauna a fili, ba a boye ba.
  20. Ta kasance mai tausayi, ba mai jawo masa bukatun da ba zai iya biya mata ba.

Babu shakka da bincike na tsanaki ne ake samun mace mai siffofi nagari abin koyi, gaggawa da kwadayi kuwa a harkar neman aure, babu abin da suke janyowa face da- na- sani, ita kuwa da- na- sani aka ce keya ce.

Ibrahim Hamisu ya rubuto ne daga Kano.

Email. ibnkhamis2 @gmail.com

08060651676