Search
Subscribe
Sinadaran Kamalar ’Ya Mace

Sinadaran Kamalar ’Ya Mace

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh; Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.  Uwargida ga abubuwan yi don kara daukaka darajarki a gidan aurenki; musamman a cikin wannan wata mai albarka don samun lada nunkin ba nunki da kuma fatan dorewa da wannn kyawawan dabi’u har bayan Ramadan; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

Sinadaran Kamalar ’Ya mace:

Kamalar ’ya mace na kunshe cikin Aya ta 34 a Suratun Nisa’i:

“To, salihan mata, masu da’a ne, masu tsarewa ga gaibi saboda abin da Allah Ya tsare.”

Daga wannan Aya mai karamci muna iya fahimtar cewa sinadaran kamalar ’Ya mace su ne:

 1. Nagarta(Salihanci)

2.Da’a.

3.Da kuma tsare dukkan abin da Allah Ya bukaci a tsare.

Wadannan siffofi a dunkule suke kuma suna dauke da rassa masu yawa fayyace su gaba daya ba zai yiwu ba a wannan shafin sai da a takaita mafi muhimmanci daga ciki.

 1. Nagartar sinadari ya samo asali ne daga nafsin dan Adam kuma ake ganinsa a bayyane a cikin halayensa, dabi’unsa da kuma yanayin mu’amalarsa; don haka dole sai nagarta ta samu a zuciya sannan take nagarta, nagartar da ake ganinta a bayyane kawai amma a zuci tsatsa ta lullbeta to wannan ba nagarta ba ce dole wata rana halayya ta canza ta nuna asalin abin da ke cikin zuciya, sannan nagartar da take a zuci amma kuma a halayya ba ta bayyana ba itama dole wata rana hali zai canza ta bayyana din. Nagarta cikakkiya ita ce wadda take a zuci kuma a zahiri cikin dabi’u da mu’amala; kamar yadda Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce Nagarta ita ce kyawun hali, haka kuma ya ce muminin da imaninsa ya kammala shi ne mai kyawun halayya. Nagarta na nufin kyawun halayya da dabi’u, wanda a takaice suna nufin mutum ya kasance mai yawan kiyayewa, mai kusanta da aikata dukkan abin kwarai abin da ya dace, kuma mai nisanta kansa da dukkan abin tir da abin da bai dace ba na tsakaninsa da Ubangijinsa, tsakaninsa da mutane da kuma tsakaninsa da al’ummar da yake zaune a cikinta. Nagartar ’ya mace shi ne ta kasance mai aikatar da dukkanin umarnin Ubangijinta a kanta da guje wa dukkan hanin Ubangijinta cikin dadin rai, hakikancewa da kankan da kai, ba a bisa al’ada kawai ba don ta ga ana yi ita ma bari ta yi; ba kuma ta rika yi a bayyane kadai ba don a ce mata saliha amma a cikin zuciyarta ba aminci. Haka nan nagarta ga miji shi ne zama da shi da alheri duka a zuci da zahiri, daukarsa a matsayin shugaba kuma jagorar rayuwa, darajtashi da girmama shi da yi masa ladabi da biyayya. Wannan shi ne gaskiyar salihanci.
 2. Da’a: Ma’anarta tana da fadi da kuma girma; tana nufin kankan da kai, yin ladabi da biyayya, saduda, neman kusanci, so da kauna, kyautata zato, tsarkake tunani, nuna so da kauna; yin kaffa- kaffa wajen zartar da al’amurra, kiyaye dokoki, aiki da hankali wajen yin mu’amula, sadaukarwa, tausasawa, kiyaye kalami, kunya, girmamawa, yarda, amincewa, girmamawa, darajtawa da sauran kyawawan al’amurra; kuma duk a yi wadannnan cikin aminci, dadin rai da sakankancewa ba tare da tursasawa ba, watau a rika yi a kan dole alhali zuciya ba ta so kuma ba ta aminta ba. A takaice dai da’a ita ce nagarta da tsarewa a aikace!

Da’ar ‘ya mace mafi girma ita ce ga Mahaliccinta Allah Madaukakin Sarki, sannan ga mijinta, sannan ga iyayenta sannan ga dukkan wuraren da ya kamata ta nuna da’a.

 1. Tsarewa na nufin tsare dokoki da umarnin Allah a kodayaushe duka na ciki da wajen aure da kuma na addini da rayuwa gaba daya. Babban abin tsarewa ga mace dai shi ne mutuncinta; Allah Ya haramta mata bayyana adonta ga duk wani namiji da ba muharrami ba, da kuma tsare amanar kanta da amanar gidan mijinta da ’ya’yan mijinta.

Wadannan sinadarai biyu da’a da tsarewa su ne tubalin ginin nagarta da kamalar ’ya mace, in ba daya daga ciki to babu kamala kuma ba nagarta.

Sai sati na gaba insha Allah inda za mu kawo muku misalai abin koyi game da wadannan sinadarai na kamalar ’ya mace.

 • facebook
 • twitter
 • whatsapp
 • linkedin