✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siriya ta mika wa Rasha hujjojin cewa ’yan tawaye ne suka kai harin mamakamai masu guba

Gwamnatin Siriya ta nuna wa Rasha hujjojin da ke nuni da cewa ’yan tawaye ne suka yi amfani da makamai masu guba, a lokacin da…

 ’Yan tawaye sun daure sojojin AssadGwamnatin Siriya ta nuna wa Rasha hujjojin da ke nuni da cewa ’yan tawaye ne suka yi amfani da makamai masu guba, a lokacin da suka kai farmaki a wajen birnin Damascus, ranar 21 ga Agustan bana. A cewar Mataimakin Ministan Harkokin Wajen, Sergei Ryabkob.
“Wadannan burbushin makamai da aka yi amfani da su an mika su ga Rasha. An sanar da mu cewa wadannan hujjoji ne da ke nuni da cewa ’yan tawaye na da hannu a wannan harin da aka kai,” inji Ryabkob kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai ya bayyana, bayan an kamala tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Siriya, Walid al-Muallem.
Ya ce Rasha za ta yi “cikakken binciken wadannan hujjoji da suka kama ’yan tawayen Siriya da laifi.”
Abin takaicin kasashen Turai, shi ne yadda Rasha ke nuna zargin cewa harin makamai amsu guba da aka kai “tunzurawa ce” da ’yan tawaye suka yi, da nufin sanya Turai ta dauki matakin soja a kan wannan rikici.
Gwamnatin Siriya na zargin manyan kasashen duniya da suka ahda da Faransa da Birtaniya da Amurka da kokarin tursasa son ransu, wajen kawar da gwamnatin kasar, inda suke nuna goyon bayansu ga ’yan tawaye. Kuma suna yi wa Majalisar dinkin Duniya matsin lamba kan lallai ta lalata makaman Siriya masu guba nan da tsakiyar shekara ta 2014.’Yan tawaye Siriya na sare kan mutum a gaban jam’a