✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sirrin da ke cikin zogale wajen magance cututtuka – Sarkin Noma

Alhaji Muhammadu Hakimin Jega, Sarkin Noma Jihar Kebbi kuma memba ne a Kungiyar Manoman Najeriya ta kasa, ya tattauna da AMINIYA inda ya bayyana muhimmancin…

Alhaji Muhammadu Hakimin Jega, Sarkin Noma Jihar Kebbi kuma memba ne a Kungiyar Manoman Najeriya ta kasa, ya tattauna da AMINIYA inda ya bayyana muhimmancin zogale ga dan Adam. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Aminiya: Me za ka ce game da daminar bana?

Sarkin noma: A halin gaskiya daminar bana tayi kyau kowace damina tana zuwa da nata yanayi, amma kusan banga wacce aka samu ruwa kamar wannan ba shi ya sa aka samu amfanin gona mai yawa, duk amfanin gonar da aka shuka a bana ya yi kyau.

Sai dai shinkafa ta noman damina taba da matsala a wuraren da ke kusa ga gulabe domin ruwa ya mamaye ta amma inda bata kusa sai hamdala kuma an samu.

Saidai kuma a nan jihar Kebbi wadansu manoma ba suyi aikin noma ba, gudun abin da ya faru bara na asarar da suka yi, gashi kuma gwamnati ba ta bayar da tallafi balle ayi noman tun da noma sai da jari.

Har yanzu nan da muke magana da kai, ban ji wani manomi da gwamnati ta ba rance don yin noman rani bana ba.

Amma da alama bana za’a samu alheri ga manoman rani da suka yi aiki kwarai da gaske don an samu ruwa a tafkuna da koguna sai dai mu yi fatan Allah yasa mu ci amfanin lafiya kuma ya sa gwamnati ta gyara ta rika ba da tallafi ga manoman gaskiya domin ciyar da kasa gaba.

Aminiya: A yanzu ga bishiyoyin zogale masu yawa a gabanka, me ka ke yi dasu haka a nan?

Sarkin manoma: Nakan kai wa wadansu ‘yan kasar Labanon ganyen zogale da kuma ‘ya’yansa. Wani lokaci a gabana sukan zo ne su wanke ganyen, sannan su nika shi har ya yi ruwa kamar jus, sannan su zuba shi a cikin jarkoki, su sanya shi a jirgi zuwa kasarsu.

Aminiya: Me su ke yi da ‘ya‘yan zogalen kuma?

Sarkin noma sun fi son ‘ya ‘yan zogalen da basu nuna ba, wadan da ba su bushe ba. Idan suka wanke su sai yanyanka su akan shinkafa su ci.

Aminiya: Mene ne amfanin zogale ga Dan adam?

Sarkin noma: Zogale na magance cutuka da dama zogale na maganin ciwon ido (Apolo). Idan wani yana fama da ciwon ido, abin zai yi shi ne ya daka ganyen zogale, sai ya diga ruwan a idonsa. Zai sha mamaki. Idan mutum na fama da ciwon ulcer, sai ya daka ganyen zogal a zuba a ruwa kadan, sannan a sha. Za a iya hadawa da madara idan ana bukatar hakan. Za a iya amfani da zogale wajen kula da hawan jini, abin da mutum zai yi shi ne, ya rikacin ‘ya ‘yan zogale biyu da safe da rana da kuma da yamma.

Idan kuma maciji ya sari wani taimakon farko da za a yi masa shi ne, misali idan maciji ya sari wani a kafa, sai a daure gefe da gefe inda macijin ya sare shi, sai ayi amfani da sabuwar reza wajen tsaga wurin da macijin ya sa reshi, sannan a zuba ruwan zogale a wurin. Daga nan za a ga dafin macijin na fitowa. Fatar bishiyar zogale na magance tsagiya. Jijiyar bishiyar zogale kuma na magance ciwon jiki. Abin da mutum zai yi shine ya yi amfani da wuka wajen kar kare jijiyar daga nan ya shanya har ta bushe. Daga nan ya hada ganye da ruwan kanwa a bari zuwa awa 24 sannan a sha. Za a iya nika ‘ya‘yan zogale daga 9 zuwa 18, a zuba a cikin kofi sannan a zuba a ruwa awa 24 kafin asha. Wannan na magance cutukan cikin fata.

Aminiya: ‘Ya‘yan zogale yana maganin ciwon siga?

Sarkin noma: mai ciwon siga zai tauna ‘ya ‘yan zogale 3 kowace safiya, idan ya juri yin hakan, zai ga abin mamaki. Za a iya ci gaba da cin abubuwa masu zaki ma ba tare da wata matsala ba. Bayan yaci gaba da cin ‘ya ‘yan zogale sai yaje wajen likita don ya auna shi, a nan zai fahimci sirrin dake cikin zogale. Ruwan zogale na fitar da gurbatattun kwayoyin halittar da ke cikin jini.

Aminiya: A gabanka akwai wadansu ganyayyaki da ba’a saba ganin su a Arewa ba, a ina ka same su?

Sarkin noma: Abubuwa da kake gani a ciki akwai albasa da alayyahu da shoko, daga kasashen waje muka shigo da irinsu, kuma muke noma wa. Shoko kamar alayyahu yake, sai dai yafi alayyahu zaki. Ba a samun sa a Arewa yana kara jini.

Aminiya: Nawa kake sayar da kilo daya na ganyen zogale da kuma ‘ya ‘yansa?

Sarkin noma: Nakan sai da zogale ga ‘yan kasar Labanon da China. Idan na auna kilo 10 na ganyen zogale sukan bani naira dubu 50. ‘Ya ‘yansa sun fi tsada. Idan ka shanya ganyen zogale a inuwa harya bushe, sannan ka daka, ka rika sa wa a miya ko kunu zaka kasance cikin koshin lafiya. Yana magance cutar maleriya da tapot.

Aminiya: Mene ne bambancin albasar da ake samu a nan Arewa da wannan da kuke nomawa?

Sarkin noma: Muna kiran albasarmu a nan ‘spring onion’, daga turanci muka shigo da irin ta. Zaka iya amfani. Da wannan albasar wajen girki, musamman idan za ka dafa kaji, tana basu dandano mai gamsar wa.

Aminiya: Wane kira za ka yi ga matasa su rungumi harkar noma?

Sarkin noma: Babbar matsalar da ta jawo talauci ya yi tsanani a yankin Arewa shi ne lalaci da mutuwar zuciya, saboda kowa yana kwadayin aikin Gwamnati.

Babu wata kasa a duniya da za ta samu ci gaba da bunkasar tattalin arziki sai ta kama noma abin da zata iya ciyar da kanta har ta sayar a kasashen duniya.

Najeriya tana daya daga cikin kasashen da Allah ya yi mata albarkar kasar noma ga ma’adanai a karkashin kasa, amma kuma matasa da dama sun yi watsi da batun noma da kiwo.

Matasa su sani babu wata gwamnati a Najeriya da za ta iya bayar da aiki ga duk wanda ya kammala karatunsa, dole sai wadansu sun rungumi aikin noma da kiwo, injishi. Babbar matsalar da ta sa talauci ya yi tsanani a tsakanin ‘yan Arewa shi ne lalaci da mutuwar zuciya domin suna da kasar noma.