✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siyasa ba ta maza ce kawai ba – Barista Jamila Babuba

Barista Jamila Babuba haifaffiyar Jihar Adamawa ce wadda ta yi aiki a Majalisar Jihar Adamawa na tsawon shekara 18. Tana daya daga cikin wadanda suka…

Barista Jamila Babuba haifaffiyar Jihar Adamawa ce wadda ta yi aiki a Majalisar Jihar Adamawa na tsawon shekara 18. Tana daya daga cikin wadanda suka jajirce wajen ganin ana damawa da mata a kowane mataki na aikin gwamnati da bangaren siyasa. Tana ma aiki da Majalisar dinkin Duniya da masu hankoron ganin ana dama da mata a ayyukan gwamnati da siyasa (UN-WOMEN). Wannan yunkurin ne ya sa aka ba ta sarautun garjajiya na Gimbiyar Njoboliyo da Jarumar Jimeta da kuma Cika Soron Adamawa. A zantawar da ta yi da Zinariya, ta bayyana tarihinta da irin gwagwarmayar da ta sha a rayuwa:

 

Tarihinta:

Sunana Jamila Babuba.  Mahaifina tsohon dan jarida ne ya taba aiki da kafar watsa labarai ta Jihar Adamawa (ABC). Sunan mahaifiyata Hajiya Asma’u Salimu ita ma tsohuwar babbar ma’aikaciya ce a Majalisar Dokokin Jihar Adamawa. Ni haifaffiyar Yola ce sannan na yi karatuna kuma na girma a cikin Jimeta. Na yi aiki a Majalisar Jihar Adamawa na tsawon shekara 18. Ina da digiri a fannin lauya a Jami’ar Maiduguri sannan na yi hidimar kasa a Majalisar Dattawa. Ni ce Daraktar kungiyar Jabu kuma a halin yanzu ina takarar neman zuwa Majalisar Wakilai don wakiltar Yola  ta Arewa da kuma Gerei.

Na yi aiki da bangaren lauyoyi kuma sau da yawa ina tsayawa a matsayin lauya ga Majalisar Jiha sannan ina aiki da Majalisar dinkin Duniya bangaren kare hakkin mata inda na kasance cikin matan da suka taka rawar gani wajen bai wa mata hakkinsu a fannoni da dama.

 

kalubalen da na fuskanta a rayuwa:

Na fuskanci kalubale da dama musamman wajen aiki da maza. Mafi yawancinsu suna kallon cewa ni mace ce don haka ba lallai ba ne tunanina ya zo daya da nasu. Ganin haka ne ya sanya na tsaya takara domin su gane cewa ba maza kadai ke da wannan damar ba. Mace ma za ta iya tsayawa kuma ta yi nasara insha Allah. Ba maza ne kadai ya kamata su rika fitowa takara ana damawa da su a harkokin siyasar kasar nan ba, siyasa ba ta maza ce kawai ba.

 

Darussan da rayuwa ta koya mini:

Rayuwa ta koya mini cewa a duk inda mutum ya tsinci kansa kada ya yi saurin yanke hukunci. Babu yadda za a yi da zarar ka kalli mutum ka ce zai iya aikata wani abu ko ba zai iya aikatawa ba. Don haka dole ne mutum ya  fahimci halin mutum tukuna kafin ya yanke masa hukuncin iya yin abu da rashin iyawarsa.

 

Nasarorin da na samu a rayuwa:

Babbar nasarar da zan iya cewa na samu a rayuwata ita ce a lokacin da na gama karatun lauya aka kira ni zuwa makarantar kwarewa ta lauyoyi. Wannan babbar nasara ce a wajena.  Idan mutum ya kasance lauya ne akwai abubuwan da yake fuskanta da dama a rayuwa, musamman ganin yana kare hakkin kowane dan Adam ne.

Nasara ta biyu kuma ita ce a lokacin da na bude kungiyata ta Jabu inda nake tallafa wa matasa wajen koyon sana’o’i. Sannan wata nasarar ita ce kokarin da nake yi na tsayawa takara a matsayina ta mace.

 

Abin da na yi sha’awar zama a lokacin da nake karama:

Ban cika kiba ba a lokacin da nake karama. Ina nan kamar Baturiya domin mahaifiyata ta ce mini a lokacin da ta haife ni mahaifina yana ta fada wa mutane cewa matarsa ta haifi Baturiya. Hakan ya sanya na ce zan zama wadda wata rana za ta lashe gasar kyau. Amma yau da gobe ta sa na zama lauya. Sannan ina sha’awar yin kwalliya da ado.

 

Burina a rayuwa:

Babban burina a rayuwa shi ne in ga ina wakiltar jama’ata a Majalisar Wakilai. Buri na biyu kuma shi ne in karo karatu kuma in samu kawaye nagari. 

 

Manhajar da nake fara dubawa da safe:

Ina fara bude manhajar ‘facebook’ idan na farka barci domin a nan nake gudanar da harkokin siyasa, inda nake tuntubar jama’ata. Kuma idan akwai gyara sai in gyara.

 

Abin kwalliya da ado da na fi so:

Ina son yin ado da ’yan kunne da sarka musamman idan na yi kwalliya. Sarka da abin wuya na kara haskaka ado. Mace tana kara kyau idan ta yi haka.

 

Abin adona da ya fi tsada:

Agogona shi ya fi tsada.

 

Inda na fi sha’awar zuwa hutu:

Ina son zuwa Dubai hutu domin akwai komai a can. Ko mene ne mutum yake son saya a duniya zai samu a can don suna da manyan shaguna. Dubai kamar wajen kasuwanci ne.

 

Yadda nake hutawa:

Idan ba na yin komai, nakan dauki wayata na yi ta duba sakonni ko kuma karanta labarai.

 

Abincin da na fi sha’awa:

Na fi sha’awar cin tuwo. Sannan ina sha’awar shan jus musamman hadin gida.

 

Turaren da na fi so:

Ina son turaren Oud da Euphoria.

Shawarar da mahaifiyata take ba ni a kullum:

Mahaifiyata mace ce mai kwazo da hazaka wajen gudanar da ayyuka hakan ya sanya ni ma na kwadaitu da wannan kyawawan halaye nata. Na san ina da hangen nesa amma a kullum duk iya kokarin da nake yi takan ce mini in kara kwazo. Mahaifiyata ta taimaka mini sosai wajen tsayawa da kafafuna. Takan sanya ni a kan hanya madaidaiciya idan ta ga na yi kuskure, sannan tana karfafa mini gwiwa.

 

Motar da na fi sha’awa:

Ina sha’awar motar kirar Range Rober Ebogue.

 

Macen da take burge ni:

Babu macen da take burge ni kamar mahaifiyata domin tsohuwar babbar ma’aikaciya ce a Majalisar Dokoki ta Jihar Adamawa ni kuma lauya. Bayan ita, Hajiya Maisaratu Bello (Zinariyar Jimeta) tana burge ni domin mace ce mai tsayuwa a kan gaskiya sannan ina son Bianca (Ojukwu) domin ta iya ado da kwalliya.

 

Kwalliya:

Ina kula da fuskata sosai amma shekin da fuskar take yi ina ganin halitta ce. Ina son yin kwalliya. kawayena suna fada mini cewa idan ban yi kwalliya ba na fi kyau.

 

Shawara ga matasa:

Ina kira ga matasa musamman mata su tashi tsaye su nemi na kansu. Kuma kada su bari wani ya yaudare su ko kuma ya sanya musu akidar cewa su mata ne don haka akwai mukaman da ba za su iya rikewa ba. Don haka ina kira ga mata su dage wajen neman ilimi domin nuna wa maza cewa su ma fa ba tayar baya ba ce a harkar gudanar da ayyuka.