Da Dumi Dumi

Siyasa fili ne komai gudunka sai ta kure ka – Lamido

Alhaji Sule Lamido
Alhaji Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya yi kira ga ’ya’yan Jam’iyyar PDP da cewa kada su bar jam’iyyar koda kuwa shi ya bar ta. Alhaji Sule Lamido ya yi wannan kira ne a wajen wani taron masu ruwa-da-tsaki da jam’iyyar ta  jihar da aka gudanar a garin Dutse.

Lamido ya kuma bukaci ’yan Kwamatin Zartawar Jam’iyyar su cike guraben da aka rasa na mukaman shugabannin jam’iyyar da wadanda suka kamata.

Ya ce, “Kamar yadda na yi shekara takwas a matsayin Gwamnan Jihar Jigawa haka shi ma Gwamna Badaru Abubakar zai yi ya gama ya koma gefe kamar yadda na zauna. Kuma zai ji yadda ake ji. Saboda kowa ya san mun yi aiki kowa ya san ba don Lamido muka yi aiki a Jihar Jigawa ba, tarayya muka yi wajen gina Jihar Jigawa, saboda haka duk mai bukatar canja sheka ya tafi yana da ’yanci, ba mai hana shi.”

Ya ce duk wani shafaffe da mai a Najeriya dan PDP ne da ya bar ta. “Kwankwaso ya fice daga cikinta, Atiku ma haka amma  ta rayu. Saboda haka  siyasa ’yanci ne kowa yana da ’yancin yin abin da yake so,” inji shi.

Sai ya hori ’ya’yan Jam’iyyar PDP su sa Jihar Jigawa a gabansu su tsaya a kan siyasar akida wadda za ta taimaka wa jihar wajen ci gaba. “Yanzu a Jihar Jigawa babu sauran jahilcin siyasa kuma kowa ya san haka saboda haka dabara ta rage wa mai shiga rijiya,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Ya shawarci jama’a su yi siyasar ra’ayi domin ita take kawo ci gaban jiha da kasa baki daya. “Babu maganar gaba a siyasa, kuma babu maganar dole, domin ita siyasa fili ce duk gudunka sai ta kure ka,” inji shi.

Share