✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siyasar Najeriya ta rasa manufa – Tanko Yakasai

Alhaji Salihu Tanko Yakasai daya ne daga cikin dattawan Arewa, Aminiya ta zanta da shi lokacin da ya ziyararci Legas inda ya yi fashin baki…

Alhaji Salihu Tanko Yakasai daya ne daga cikin dattawan Arewa, Aminiya ta zanta da shi lokacin da ya ziyararci Legas inda ya yi fashin baki kan al’amuran siyasa da hanyoyin da za a bi domin ci gaban kasa:

 

Yaya kake ganin salon siyasar kasar nan a wannan lokaci?

Salon siyasar Najeriya yanzu a gurbace yake, saboda ita siyasa ana yin ta ce ta kan jam’iyya ita kuma jam’iyya ita ce matattarar mutane masu ra’ayi iri daya. Manufar yin jam’iyya ita ce mutane masu ra’ayi iri daya su shiga jam’iyya su yi manufa iri daya idan sun nemi gwamnati, ranar da suka samu gwamnati su aiwatar da wannan manufa don su gyara kasa. Da aka fara siyasa da manufa aka fara, amma yanzu babu manufa a jam’iyya, jam’iyya yanzu ba ta da ’ya’ya. A baya ’ya’yan jam’iyya su ne jam’iyya, ba wanda zai shiga wani shugabanci na kasa ko na jam’iyya sai ’ya’yan jam’iyya sun zabe shi, amma yanzu ba ’ya’yan jam’iyya ke zaben wanda zai shiga zabe ba, ba su ne suke zaben wanda zai zamo Shugaban Kasa ko na jiha ko karamar hukuma ba, ba su ne suke zaben wanda zai shugabanci jam’iya ba, a’a kudi ne yake zaben wadannan mutane. Duk wanda ya zo neman zabe ba mutane yake nema ba, kudi yake zuwa da su makil in ya raba ya samu biyan bukata, zai yi lissafin abin da ya kashe kuma ya yi fatar wannan mukami da ya samu ya yi amfani da shi ya mayar da kudin da ya kashe har ya samu riba. Saboda haka yanzu siyasa ta lalata kanta, ta kuma lalata kasuwanci da sana’a domin idan mutum ya yi kasuwanci ya samo kudinsa, maimakon ya zuba jari a kasuwanci ya kara karfin jari sai ya kawo kudin ya shiga siyasa da su domin a nan ake samun kudin banza! A nan za ka ga mutum ya zo ba ya da ko dari amma ya zamo mai miliyoyin Naira, saboda haka siyasa ta lalace.

Wace hanya kake ganin ya kamata a bi a gyara wannan matsala?

Ba za a gyara kasar nan ba sai an gyara siyasa, abin da kuma zai gyara siyasa shi ne jam’iyya ta zama ta ’yan jam’iyya, su za su yanke hukunci kan wanda zai tsaya takara a kowane mataki, su za su ja ragamar jam’iyya. To idan wannan iko ya dawo hannun talakawa daga nan za a zabi mutane a kan dacewa ba a kan kudinsu ba. Matukar ba haka aka yi ba, kasa ci gaba za ta yi da lalacewa. Babbar matsalar ita ce wadanda ke zuwa su samu mulki ba su da manufa sai don kabilanci ko don kudin da suke da shi.

Ka zo Legas a daidai lokacin da wadansu ’yan Arewa suke kokawa cewa hukumomin jihar na uzzura musu. A matsayinka na dattijo daga Arewa me za ka ce game da wannan?

To ’yan Arewa a Legas ba ma a Legas kadai ba, a ko’ina har a Arewar, ya kamata su samu manufa yanzu. A daina tunanin ai ni dan Arewa ne, eh haka ne, kai dan Arewa ne, amma me ka yi wa Arewar ko me za ka yi mata? Ko kuma kai dan Najeriya ne to me ka yi wa kasar? Gadara babu manufa ta zama aikin banza.

Kana ganin akwai bukatar taron kasa domin magance wannan matsala?

An dade ana shirya taron kasa tun a lokacin Turawa, amma har yanzu taron kasa bai fidda abin da kasa ke bukata ba. A samu mutane masana daga kowane bangare wadanda za su fito da abin da zai magance mana matsalolin da kasarmu ke fama da su. Wadanda za su fitar da takarda dauke da manufofin da za su kai kasar nan gaba. Na je taron kasa ya fi sau uku, da yawa wadanda ke zuwa ba sa zuwa da wata shawara, taron kasar da na je a karshe da na lura idan na fito da ra’ayina ’yan uwana ma ’yan Arewa za a samu matsala da su, sai na je na samu shugabannin kwamitin taron kasar na ba su shawarwarin da ke zuciyata, a karshe an samu shawarwarina guda bakwai da aka yi amfani da su. Saboda haka ba magana ce ta a kawo mutane daga Katsina ko daga Kano ko Legas ko Kaduna ba, a’a a tattaro masana daga wadannan yankin domin su fito su bayyana manufofin da za a bi a samu ci gaba a kasar nan domin kasar ta balbalce tana kuma bukatar irin wannan taro.

Me kake gani ya kamata a mayar da hankali a kai don magance matsalolin kasa?

Yanzu abin da ke damun kasar nan shi ne talauci da jahilci. Hanya mafi sauki na maganin talauci shi ne noma, domin idan akwai kyakkyawan tsari na noma cikin shekara biyu kadai za a samu gagarumin ci gaba. Idan da akwai wutar lantarki isasshiya cikin shekara daya zuwa daya da rabi mutane za su samu ayyukan yi, domin hanyoyin bukasa tattalin arzikin kasa ke nan noma da masana’antu. Kuma ba za ka bunkasa aikin noma ba sai ka sauya tsarin noma, wato hanyar noma ta zamani da kayan aiki da takin noma domin ko a baya can da taki ake takama wajen noma. A samu wutar lantarki, a baya can lokacin da ake da isasshiyar wutar lantarki akwai cibiyoyin masana’antu uku a Arewa daya a Kudu wato a Arewa akwai Kano da Kaduna da Jos, sai Legas a Kudu, Kudu a baya jiha daya ce kadai ta kai wannan mataki amma a yanzu da mu da Kudun duk mun gurgurce saboda rashin wutar lantarki. Kuma in ba wannan gyara aka yi ba, a kullum kasar nan za ta ci gaba da kasancewa cikin talauci.