Search
Subscribe
Soja ya kashe sojoji 4 ya harbe kansa                                                                                                                                            

Soja ya kashe sojoji 4 ya harbe kansa                                                                                                                                            

Wani soja da ke aiki da rundunar Lafiya Dole wadda ke yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas, ya kashe abokan aikinsa hudu, sannan ya harbe kansa.

Wata sanarwa da Mukaddashin Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Kanar Sagir Musa, ya aike wa manema labarai shekaranjiya Laraba da yamma ta ce sojan, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya kuma jikkata wadansu abokan aikinsa biyu.

Sanarwar ta kara da cewa rundunar sojin tana kokarin tuntubar iyalan sojojin da aka kashe.

A cewar Kanar Musa, rundunar sojin Najeriya ta fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano abin da ya haddasa shi hallaka abokan aikinsa da kuma kansa.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin