✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soja ya kashe yarinya da dabawa dan sanda wuka

Ana tuhumar wani soja da laifin kashe wata yarinya da kuma dabawa dan sanda wuka a Maiduguri. Lamarin dai ya faru ne a daren jiya…

Ana tuhumar wani soja da laifin kashe wata yarinya da kuma dabawa dan sanda wuka a Maiduguri.

Lamarin dai ya faru ne a daren jiya Litinin lokacin da aka yi wata tarzoma har zuwa wayewar garin safiyar yau Talata a kusa da kasuwar Wulari Police Mammy, a wata mashaya da misalin karfe 7:30 na dare.

Wani ganau ya ce, yana wurin lokacin da yaga wasu mutane su uku su na ta dukan wata yarinya wanda yake tunanin budurwar daya daga cikinsu ne, saboda taki amincewa da tabi daya daga cikin mazan a Keken Napep dake harabar mashayar.