Search
Subscribe
Sojan bogi da ya farke mazakuntar wani ya shiga hannu

Kazeem Ali, sojan bogi

Sojan bogi da ya farke mazakuntar wani ya shiga hannu

Wani sojan ruwa na bogi da ake zargi da yunkurin yin kisa ya shiga komar ’yan sanda a Legas.

Wanda ake zargin mai suna Azeez Ali mai shekara 40 da ke zaune a gida mai lamba 5 a Unguwar Morgan a yankin Igando ya shiga hannu ne bayan ya yi yunkurin kashe wani mutum mai suna Sunday Amoo  bayan  takaddama a tsakaninsu.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa wanda ake zargin ya yi amfani da  wukar soji ya farke wa abokin fadansa Sunday Amoo mazakunta, sannan ya ce an kama wanda ake zargin ne a Tahsar Motar Berger, “Wanda ake zargin yana sanya kayan sojin ruwa inda yake yi wa jama’a barazana cewa shi sojin ruwa ne, ya yi wa mutumin da suka yi sa-in-sa mummunan yanka a mazakuntarsa, wanda zuwa yanzu ake kokarin ceto ransa a asibiti inda ake ba shi kula ta musamman,” inji shi

DSP Bala Elkana ya ce ana ci gaba da bincike kuma za a gabatar da wanda ake zargin a gaban kotu domin ya fuskanci shari’a.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin