✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojin Amurka sun tabbatar da hadarin jirgin sama, sun musanta kakkabo jirgin

Sojojin Amurka sun tabbatar da daya daga cikin jiragen rundunar a gabashin lardin Ghazni a Afghanistan ya yi hadari ranar Litinin, amma sun karyata ikirarin…

Sojojin Amurka sun tabbatar da daya daga cikin jiragen rundunar a gabashin lardin Ghazni a Afghanistan ya yi hadari ranar Litinin, amma sun karyata ikirarin cewa, kakkabo jirgin aka yi, a wani hari da masu tada kayar baya suka kai.

“Yayin da ake ci gaba da gudanar da binciken musabbabin hadarin, babu wasu alamu da ke nuna cewa hadarin ya faru ne sakamakon harin da abokan gaba suka yi,” in ji wani kakakin sojin Amurka Kanal Sonny Leggett, cikin wani jawabi da ya fitar.

Da yake tabbatar da rahotannin wani dauki ba dadi da aka yi, Zabiullah Mujahid, wani kakakin ‘yan gwagwarmayar Taliban, ya ce sojin Afghanistan da ke samun goyon bayan sojin Amurka sun yi yunqurin kwace ikon yankin da ya ce sun kakkabo jirgin Amurka.

Sai dai ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, za su kyale jami’an agajin gaggawa su shiga yankin da abin ya faru  domin daukar gawarwakin wadanda hadarin ya rutsa da su.