✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji 9 sun mutu a hatsarin jirgin sama

Wasu jiragen sama masu saukar ungulu guda biyu sun yi taho-mu-gama da juna a lardin kudancin Helmand na Afghanistan

Wasu jirage masu saukar ungulu guda biyu sun yi taho-mu-gama tare da kashe mutum tara da ke cikinsu a lardin Kudancin Helmand na Afghanistan.

Ma’aikatar Tsaron kasar ta ce hatsarin ya faru ne a ranar Laraba sakamakon tangarda da jiragen suka fuskanta jim kadan da tashinsu.

Ma’aikatar ta ce tana nan tana ci gaba da bincike domin gano hakikanin musabbabin hatsarin.

Wasu majiyoyi a yankin sun tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labarai na DPA cewa jiragen sun yi hatsarin ne lokacin da suke kokarin ceto sojojin da suka samu raunuka a filin daga a yankin Nawa mai fama da rikici wanda hakan ya tilasta musu yin kaura daga yankin cikin gaggawa.

Kafafen yada labaran yankin sun ruwaito cewa sojojin na kokarin kai tallafi ne ga takwarorinsu a yankin tare da kwaso wadanda suka jikkata daga cikinsu.

Kusan  mako daya ke nan mayakan kungiyar Taliban na kai hare-hare a yankunan kudancin kasar, ciki har da birnin Lashkargah.

’Yan tawayen sun katse wutar lantarkin da ta hada birnin tare da tayar da bama-bamai a mashigarsa, yayin da dakarun gwamnati ke yin luguden wuta ta sama da kasa.

Rikicin ya yi sanadiyyar kashe sojoji da fararen hula da dama, ko da yake ba a kai ga tantance adadin wadanda lamarin ya shafa.

Akalla mutum 35,000 suka yi kaura daga yankin na Helmand a ’yan kwanakin nan.

Majalisar Dinkin Duniya, a ranar Talata ta yi hasashen cewa sama da mutum 200 sun mutu ko kuma sun jikkata sakamakon wani mummunan harin da Taliban ta kai a kasar.