ADVERTISEMENT

Sojoji na horar da jami’an Kwastam sarrafa makamai a Bauchi

Sojojin Najeriya sun fara horar da jami’an Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya, Kwastam su dubu 2 yadda za su iya sarrafa bindigogi da wasu makaman tsaro.

Rundunar sojojin da ke barikin Shadawanka a jihar Bauchi, ta fara horar da jami’an Kwastam din ne da ke shiyya ta Zone D a jihar.

ADVERTISEMENT

Shiyyar Zone D ta hada da jihohin: Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba, Borno,  Yobe, Benue, Nassarawa da jihar Filato.

Kwamandan rundunar sojojin kuma wanda yake jagorantar horarwar Birgediya Janar Michael T. Durowaiye, ya ce horarwar da aka shiryawa jami’an Kwastam din zai taimaka wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

ADVERTISEMENT