✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun cafke ’yan bindiga 150 a wurin hakar zinare

An kwace bindigogi da yawa a hannun 'yan bindigar da suka mayar da wurin maboyarsu

Rundunar soji ta Operation Sahel Sanity ta cafke  mutum 150 da zargin fashin daji a wani simame da ta kai wani wurin hakar ma’adanai a Jihar Zamfara.

Babban jami’in sadarwa na rundunar, Birgediya Benard Onyeuko, sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce ’yan dabar dajin da aka kwace kananan bindigogin hannu 20 a wurinsu na amfani da wurin a matsayin mafaka.

Ya ce an mahakar ma’adinan da aka kama mutanen na yankin Gadan Zaima na Karamar Hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara.

Haka kuma a sintirin da dakaru suka saba gudanarwa, sun yi arangama da yan bindiga uku a kan babura a kusa da kauyen Maigama na Karamar Hukumar Anka suna shirin kai wa mazauna kauyen hari.

A yayin artabu, sojojin sun kashe dan ta’adda daya, yayin da ragowar biyun suka arce da kafafunsu tare da zubar ba makamansu ciki har da bindigogi kirar AK-47 da kuma alburusai da dama.

Birgediya Benard ya kara da cewa, wani jagoran ‘yan daban daji mai suna Bornon Kejo, ya mika wuya ga dakaru a Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar, ya kuma ajiye makamansa na yaki da suka hadar da bindigogi biyu kirar Ak-47 da alburusai.

Sojoji sun kuma datse wasu motoci bakwai makare da shanu a babbar hanyar Jibiya zuwa Katsina da kuma hanya Gusau zuwa Zariya wanda ake na sata ne.

A yanzu haka dai an mika shanun a hannu rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina domin daukar matakin da ya dace.