✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun ce su gwabza da mayakan kabilar Bassa a Nasarawa

A karshen makon jiya  ne sojoji a Jihar Nasarawa suka kai hari ga mayakan kabilar Bassa a kauyen Zwere da ke Karamar Hukumar Toto a jihar,…

A karshen makon jiya  ne sojoji a Jihar Nasarawa suka kai hari ga mayakan kabilar Bassa a kauyen Zwere da ke Karamar Hukumar Toto a jihar, inda sansanin mayakan yake suka kwato manyan bindigogi 45 da layu da wasu makamai da suka kai guda 701.

Kwamandan sojojin da suka kai wa mayakan harin, Major Janar Adeyemi Yekini ne ya sanar da haka lokacin da yake gabatar da makaman da suka kwato daga mayakan ga manema labarai a Sakatariyar Kungiyar ’Yan jarida ta jihar da ke Lafiya jim kadan bayan musayar wutar.

Kwamandan ya ce mutanensa sun yi wa mayakan kwanton-bauna ne a kauyen Ugya da ke Toto inda suka fara bude musu wuta kafin daga bisani a cewarsa mayakan su tsere da munanan raunuka a jikinsu.

“Da muka samu labarin cewa mayakan suna da sansani a kauyen Zwere sai nan take muka kai musu farmaki inda muka fara musayar wuta da su tun ranar Juma’a har zuwa Asabar. Bindigogi da layu da sauran makamai da muka kwato guda 39 da kananan bindigogi 3 da wayar salula guda 2 da jigidar harsasai da bindiga kirar AK 47 guda 1 da sauransu,” inji shi.

A cewarsa Rundunar Sojin Kasa  da hadin gwiwar kasashen waje ne suka ba da umarnin a rika tunkarar kungiyoyin ta’adda a jihar da kasa baki daya don kawo karshen kashe-kashen da a cewarsa wadansu Fulani makiyaya da mayakan kabilu ke ci gaba da yi a wasu kauyuka a jihohin Nasarawa da Benuwai da Taraba da kewayensu.

Sai dai a nasu bangaren  kabilar Bassa inda lamarin ya auku, sun musanta zargin da sojojin suka yi cewa kabilarsu na da sansani a kauyen.

Shugaban Kungiyar Ci gaban Al’ummar Bassa ta Kasa, Gwatana Huleji Dogwo ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu dangane da aukuwar lamarin.

Ya ce “Ka ga wannan sanarwa da sojoji suka yi wa ’yan jarida sun yi ne don su boye wa al’umma gaskiyar lamari. Sun hada baki da wadansu mayakan kabilar Ebira ne sun kai hari a kauyen suka kashe mana mutane da dama. Don wannan kauye na Zwere inda sojojin suka kai hari daya ne daga cikin kauyukanmu na al’ummar Bassa da suka rage a Toto, kuma ba sansanin mayakan kabilar Bassa ba ne. Kuma duk makamai da sauransu da suka ce sun kwato wajen mayakan Bassa ba gaskiya ba ne.”

“A yanzu da muke magana al’ummarmu suna gudun tsira da rayuwarsu ce sakamakon hare-haren da mayakan kabilar Ebira ke kai mana a kai-a kai. Ta yaya za mu iya kafa sansani a kauyen? Mu dai al’ummar Bassa mun tabbata wadannan sojoji sun hada baki ne da kabilar Ebira da muke fada da su don su kawar da mu baki daya daga doron kasa.  Ina so in yi amfani da wannan dama a madadin al’ummar Bassa a Karamar Hukumar Toto da jihar nan baki daya in yi kira ta ga gwamnatoci a dukan matakai da Rundunar Sojin Kasa da kuma duniya baki daya su san da abin da ke faruwa. Ya kamata rundunar sojin ta gudanar da bincike a kan sojojin da suka kai mana hari a kauyen inda suka rika harbin duk wanda suka gani tare da kone mana dukiyoyi,” inji shi.