✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Adamawa

Rundunar sojojin Najeriya ta ce, dakarunta sun dakile harin ‘yan Boko Haram a karamar hukumar Michika jihar Adamawa. Kakakin rundunar sojojin Najeriya Kanal Sagir Musa…

Rundunar sojojin Najeriya ta ce, dakarunta sun dakile harin ‘yan Boko Haram a karamar hukumar Michika jihar Adamawa.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya Kanal Sagir Musa ne ya sanar da hakan, inda ya ce ‘yan Boko Haram sun yi yunkurin kai hari a garin Michika amma daga bisani sojojin suka yi nasarar dakile harin.

`Yan kungiyar sun yi yunkurin tserewa lokacin da suka shirya ke harin amma dakarun suka bude masu wuta wanda hakan yasa suka ci galaba akan su.