✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun dakile harin Boko Haram sun kashe 39

Rundunar hadaka ta dakarun kasashe da ke yaki da ‘yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, MNJTF, sun kashe mayakan Boko Haram 39 tare da…

Rundunar hadaka ta dakarun kasashe da ke yaki da ‘yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, MNJTF, sun kashe mayakan Boko Haram 39 tare da kwato makamai masu yawa a hannun su, a yayin arangamar sojoji 20 sun samu raunuka.

Kakakin rundunar sojojin Kanal Timothy Antigha, ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da yake ganawa da manema labarai jiya Laraba a Abuja.

Kanal Timothy, ya ce an kashe maharani ne a yankin Cross Kauwa jihar Borno ranar Talata yayin da wadanda aka raunata yanzu haka suke asibiti suna jinya.