✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun fara zawarcin dalibai masu sha’awar aikin soja a Jigawa

Ritaya da yaki da Boko Haram sun sa Najeriya tana fuskantar karancin sojoji, wanda hakan ya sa gwamnati ta umarci manyan sojojin kasar nan su…

Ritaya da yaki da Boko Haram sun sa Najeriya tana fuskantar karancin sojoji, wanda hakan ya sa gwamnati ta umarci manyan sojojin kasar nan su zagaya wasu makarantun Najeriya da suka yi fice wajen cin jarrabawar karshe domin tallata bukatarsu ga dalibai masu sha’awar shiga aikin soja.

Wani babban soja, Kwamanda James Aliyu Pinder ya jagorancin ayarin sojojin zuwa Jihar Jigawa inda suka je makarantun kimiyya da na sana’a da ke Ringim da Dutse da Model International da Makarantar Sakandaren Wunti da ke Hadeja.

Da yake jawabi, Kwamanda James ya ce makasudin zuwansu Jigawa shi ne su nuna bukatar da ke akwai ta yara su rika shiga aikin soja.

Ya ce shiga aikin soja ba wani abu ne mai ban tsoro ba matukar an ci jarrabawa. Ya ce abin da ake bukata shi ne daliban su samu nasara a darasi biyar ciki har da Ingilishi da lissafi, sannan ya ce komai kyauta ne, babu bukatar kudi.

Kwamanda James ya ce umarni ne aka ba su daga Fadar Shugaban Kasa su zagaya fitattun makarantun sakandare a fadin Najeriya da nufin samar da kwararrun sojoji masu kwazo da Najeriya za ta yi alfahari da su nan gaba.

Daga nan sai ya koka game da yadda daliban suke fuskantar karancin fadakarwa game da yadda ake shiga aikin soja ko shiga makarantar horar da kananan hafososhin soja (NDA).

Ya ce da zarar dalibi ya samu nasarar shiga NDA, komai kyauta ne ba maganar kudi ko kayan karatu ko biyan kudin kiwon lafiya, inda ya ce duk gwamnati ce za ta dauki nauyin komai.

Ya ce za su dauki dalibai 200 daga kowace jiha daga cikin makarantun da aka zaba da suka ziyarta a daukacin jihohin 36 da ke Najeriya, don haka ya bukaci daliban da suke da sha’awar shiga soja a daukacin makarantun da su dage sosai su samu nasara a jarrabawarsu ta kammala sakandare.

Sannan ya hori daliban da su guji shaye-shaye miyagun kwayoyi, domin hakan yana lalata rayuwar matasa.

Da yake jawabi, Kwamashinan Ilimi na Jihar Jigawa, wanda wani darakta Malam Wada Abdullahi daga Ma’aikatar Ilimi ta Jihar ya wakilta, ya ce akwai bukatar daliban su saurari bayanan da aka gabatar sosai kuma su yi amfani da abin da aka fada musu.

Shi ma Shugaban Makarantar Dutse Model International Malam Lawal Adamu Yusuf ya ce makasudin zuwan sojojin makarantar shi ne saboda umarnin da Gwamnatin Tarayya ta ba su na su zagaya daukacin makarantun jihohi 36 da aka zaba domin a samar da zaratan sojoji masu hazaka a Najeriya.