✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun fatattaki ’yan bindiga a Nasarawa da Biniwai

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta yi wa ’yan bindiga da bayarin shanu kwanya a Yankin Arewa ta tsakiya inda ta samu nasarar kame hudu…

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta yi wa ’yan bindiga da bayarin shanu kwanya a Yankin Arewa ta tsakiya inda ta samu nasarar kame hudu daga cikin ’yan bindigar ta kuma gano bindigogi da albarusai a lokacin samamen a sansanin su biyu da ke yankin.

Mai Magana da yawun Rundunar Manjo Janar John Enenche, a wata sanarwa da ya fitar ya ce, a daya daga cikin samamen da rundunar ta kai ranar 6 ga watan Satumbar 2020, rundunar da ke Guma a Jihar Biniwai da Keana a Jihar Nasarwa, ta kai farmaki ga ’yan bindigar a sansaninsu da ke dajin Guma kan iyaka da Biniwai bayan bayanan sirri da suka samu a kan mabuyar ta su.

Ya bayyana cewa, sun dirar wa ’yan ta’addar da lugudan wuta inda suka fafata da su kafin daga baya su ci karfin ’yan bindigar da manyan makamai.

Ya ce a cikin gumurzun rundunar sojin ta hallaka mutum guda daga cikin ’yan bindigar, inda wasu suka gudu cikin daji da raunuka.

Ya kara da cewa rundunar ta gano bindiga kirar Ak-47 da kwanson harsashi daya da bindiga kirar gida da wayoyin hannu ukku an kuma wargaza sansanin.

Jami’in ya ce rundunar ta dirar wa maboyar ’yan bindigar inda suka cafke mutum hudu da ake zargi da bindiga kirar Ak 47 da kwanson harsashai da wasu masu jigida wanda aka samu a mabuyar ta su.