✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun gudu da miliyoyin kudin kwamandansu

Rundunar Sojojin Najeriya ta soma gudanar da bincike a kan wata tuhuma da ake yi wa wadansu jami’an soja bisa zargin gudu da wasu miliyoyin…

Rundunar Sojojin Najeriya ta soma gudanar da bincike a kan wata tuhuma da ake yi wa wadansu jami’an soja bisa zargin gudu da wasu miliyoyin kudade da ke cikin motar da aka umarce su yi wa rakiya daga Sakkwato zuwa Kaduna.

Rundunar ta bayyana sunayen jami’an da ake zargi da guduwa da miliyoyin Naira wadanda suka hada da Kofur Gabriel Oluwaniyi da Kofur Muhammad Aminu da Las Kofur Haruna da  Las Kofur Oluji Joshua da kuma Las Kofur Hayatudeen. Rundunar ta ce dukkansu sun fito ne daga Runduna ta 8 da ke Sakkwato  da ke gudanar da shirin Harbin Kunama III, a Arewa maso Yamma.

Kakakin Runduna ta 8 da ke Sakkwato, Laftana Audu Arigu ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce “Bincike ya yi nisa domin zakulo sojojin da ake zargi da gudu da wadannan kudade.”

Sai dai rundunar ta ki bayyana sunan kwamandan da ya mallaki makudan kudin da jam’ian suka gudu da su. Amma wata kwakkwarar majiya wacce take da masaniyar yadda abin da ya faru ta shaida wa Aminiya, a daren Lahadin da ta gabata, cewa wanda ake alakantawa da kudin shi ne Manjo Janar Hakeem Otiki, Kwamandan Runduna ta 8 da ke Sakkwato (an yi masa sauyin wurin aiki.

Majiyar ta ce sabanin abin da rahoton ya ce, Kwamandan ba ya tare da ’yan rakiyar. Ya dai tura su ne kawai saboda ya yarda da su.

Daga cikin wadanda ake zargi da gudu da kudin, an kama mutum biyu, kamar yadda majiyar ta sce. “Kamar yadda yake faruwa a aikin soja, kowane babban jami’in soja yana da jami’an da ya amince da su, a wani lokacin ma sama da iyalansa. Abin da ya faru da Kwamanda ke nan a nan Sakkwato. Ya amince da su, su kuma suka arce da makudan kudin” inji majiyar.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “Hakika biyu daga cikin wadanda ake zargi sun shiga hannu, sannan ragowar ma akwai yiwuwar nan gaba kadan a kamo su. Ba zan fadi sunayensu ba amma na san nan gaba kadan hukumar soja za ta sanar da sunayen wadanda aka kama.

“Sun riga sun tona wani asiri da watakila ka iya janyo mutane da yawa su shiga cikin wannan al’amari, domin za a tambaye su daga ina suka samo wannan izini na raka wannan kudi kuma ina za su kai su da sauran tambayoyi masu yawa.

Aminiya ta gano cewa kafin a maida Kwamandan zuwa Sakkwato, shi ne yake rike da Barikin Soja na Jaji da ke Jihar Kaduna. Haka kuma ta samu labarin cewa, dukkan jami’an da ake zargi, sun fito ne waje daya da Kwamandan, wato Barikin Jaji da ke Kaduna. Lokacin da aka yi wa Kwamandan sauyin aiki, sai ya  nemi a yi wa wadannan jami’ai sauyin aiki zuwa inda yake a Sakkwato.