✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun harbi ‘barayin abinci’ a sansanin NYSC na Abuja

Mutum biyu sun sha dalma wasu 41 kuma na tsare a hannun jami'an tsaro

Sojoji sun harbi mutum biyu tare da tsare wasu 43 da suka fasa rumbuna ajiyar kaya da ke sansanin Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC) da ke Kubwa a Abuja.

Sojojin sun yi harbi ne tare da wartakar mutanen bayan daruruwan matasa sun yi wa sansanyin tsinke a ranar Talata da cewa sun neman kayan tallafin COVID-19 sun yi kukan kura sun yi kansu.

“A lokacin ne sojoji suka harbi mutum daya a kafa, wani kuma a hannu wadanda aka garzaya da su zuwa asibiti”, inji wani ganau.

Ya ce da farko ‘yan sanda sun kai wa wurin dauki amma matasan suka fi karfinsu.

Darakta-Janar na Hukumar NYSC, ya tabbatar wa Aminya cewa an damke 41 daga cikin wadanda aka zargi a lamarin, sai dai ya ce ba shi da masaniya kan wadanda aka harba.

Ya yi takaicin aukuwar hakan a daidai lokacin da hukumar ke shirin bude sansanoninta domin ci gaba da horas da matasan da suka kammala karatu.

“Buhunan shinkafa da matasan suka sace sun kwasa ne daga dakin ajiyar abincinmu da suka rage daga shirinmu na baya wanda aka dakatar baya mako daya da farawa saboda bullar annobar COVID-19”, inji shi.

Baturen ‘yan sanda da yankin Kubwa, CSP Bello Abdullahi ya ce akalla mutum 30 daga cikin wadanda ake zargi na tsare kafin a wuce da su zuwa sashen binciken manyan laifuka sannan a gurfanar da su a kotu.

  • Ci gaba da fasa dakunan ajiya

Matasan sun kutsa ma’ajiyar sansanin NYSC din ne bayan sun fi karfin mai gadin da ke wurin inda suka rika debo takalma, kaki, tufafi, katifu da kayan koyon sana’a.

Sun kuma yi awon gaba da tukwane, janaretoci, babura, kwamfutoci, da sauran kayan ofis a wurin.

Hakan ya auku ne bayan an farfasa wasu rumbunan ajiyar kayan abinci da na agajin gaggawa a Abuja.

  • An fasa sansanin NYSC na Abuja

A safiyar Talata ne wasu bata gari suka haura sansanin masu yi wa kasa hidima dake Kubwa a Abuja.

Mutanen dauke da muggan makamai sun tare hanyar shiga sansanin, tare da hana masu babura wucewa.

Matasan tare da wasu mazauna yankin sun haura cikin sansanin inda suka tare sojan da ke gadi, kuma an hange su suna fitowa da katifu da sauran kayan amfanin masu yi wa kasa hidima da ke sansanin.

Kwana uku ke nan a jere bata-gari na fasa rumbuna ko wasu kayan gwamnati da sunan neman kayan tallafin annobar COVID-19 a Abuja.

A ranar Lahadi sun fasa rumbunan ajiya dake rukunin masana’antu da ke Idu da na Jabi Daki-Biyu, sannan a ranar Litinin suka fasa rumbun abincin tallafi da ke Gwagwalada.

Yanzu haka dai yanayin ya fara canja salo zuwa sata, yayin da hakan ta ke faruwa kan wanda basu ji basu gani ba.