✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe barayi 55 da kubutar da mutum 760 a Zamfara

Rundunar sojojin Najeriya na Operation Sharan Daji sun kashe barayi masu garkuwa da mutane 55 tare da kubutar da mutum 760 da aka yi garkuwa…

Rundunar sojojin Najeriya na Operation Sharan Daji sun kashe barayi masu garkuwa da mutane 55 tare da kubutar da mutum 760 da aka yi garkuwa da su a kauyukan jihar Zamfara.

Mukaddashin jami’in sadarwa na rundunar sojojin Manjo Clement Abiade ne ya sanar da hakan a Gusau babban birnin jihar Zamfara, ya kuma ce rundunar ta yi nasarar kwato makamai daga hannun barayin sun toshe duk wasu hanyoyi da barayin ke amfani da su.

Dazukan da rundunar takai samame sun hada da: Kagara, Gando, Fankama, Fete da Dumburum.