✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe barayi da masu garkuwa a Kaduna

A shirin yakin da Rundunar sojojin Najeriya suke yi da masu tada zaune tsaye wanda aka yi wa lakabi da ‘Operation Whirl Punch’ wanda hakan…

A shirin yakin da Rundunar sojojin Najeriya suke yi da masu tada zaune tsaye wanda aka yi wa lakabi da ‘Operation Whirl Punch’ wanda hakan ya sa aka kashe barayin shanu da masu garkuwa da mutane a dajin Kamuku, a karamar Hukumar Birnin Gwari jihar Kaduna.

A wata sanarwa da mataimakin Daraktan jami’in hulda jama’a na rundunar sojojin  Kanal Muhammad Dole, ya ce a yayin farautar masu laifin ranar 9 ga Oktoba sun kwato muggan makamai da bindigogi kirar AK 47 a hannun maharan tare da raunata wasu da dama.