✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram

Rundunar Tsaron Najeriya ta yi ikirarin hallaka kwamandoji da mayakan Boko Haram da dama a sansanoninsu da ke Karamar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno a…

Rundunar Tsaron Najeriya ta yi ikirarin hallaka kwamandoji da mayakan Boko Haram da dama a sansanoninsu da ke Karamar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno a gabar tabkin Chadi.

Jami’in yada labaran rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya ce sojoji sun ragargaza sansanonin “Yan ta’adda a Tunbun Gini da Tunbun Nbororo da Tunbun Kayoma da Tunbun Kaza da kuma Tunbun Fulani a hare-haren da suka kai.

“Kwamandojin Boko Haram din da ya ce sojoji sun kashe sun hada da Abu Usman da Alhaji Shettima da Modu Mainok da Bukar Gana da Abu Summayya da Amir Taam da kuma Amir Kuraish,” inji shi.

Enenche ya bayanna kwarin gwiwar cewar sojojinda taimakon sauran jami’an tsaro za su yi bakin kokarinsu wajen kawo karshen ta’adanci da sauran laifuka a kasar.

“Muna kara tabbatar wa mutanen Arewa maso Gabas cewar sojojin na bakin kokarinsu domin kare musu lafiya da dukiyoyinsu.

“Muna kuma kira gare su da su rika samar wa jami’an tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen aikinsu”, kamar yadda ya bayyana.