✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe masu garkuwa 2 da kwato bindigogi a Kaduna

Rundunar sojojin Najeriya  na  Division 1 a Kaduna  sun ce sun yi nasarar bankado maboyar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a gabashin Gonan Bature…

Rundunar sojojin Najeriya  na  Division 1 a Kaduna  sun ce sun yi nasarar bankado maboyar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a gabashin Gonan Bature a garin Rijana da gidan gona na Kasarami da ke karamar hukumar  Chikun a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar sojojin Kanal Sagir Musa ne ya sanar da hakan a jiya Laraba da daddare, ya ce sun yi nasarar gano maboyar ‘yan bindigar ne ta hanyar bayanan sirri daga wani mazaunin yankin.

Gidan gona na Kasarami wanda ya zama kango ya kasance wajen da masu garkuwa da mutane ke amfani da shi don ajiye wadanda suka kama.

An yi musayar wuta da ‘yan bindigar kafin daga bisani sojojin su kwato bindigogi biyu kirar AK 47, mujallar bindigogin AK 47 da alburusai 51 da wayar sadarwa guda biyu.