✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 20

Sojojin Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram guda 20 sannan suka kame wasu a Monguno, jihar Borno. Dakarun sun kuma kwace motoci da makaman maharan…

Sojojin Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram guda 20 sannan suka kame wasu a Monguno, jihar Borno.
Dakarun sun kuma kwace motoci da makaman maharan a ranar Asabar, sadda suka yi nasarar dakile harin ‘yan kungiyar.
Kakakin Rundunar Tsaro ta Najeriya Manjo Janar John Enenche ya ce mayakan sun gamu da gamonsu ne a hannun dakaru da jiragen yakin rundunar Operation Lafiya.
Sanarwar da ya fitar ta ce sojojin sun nuna kwarewa da bajinta a garin na Monguno kuma suna da kwarin gwiwar ci gaba da fatattar ‘yan ta’addan ta sama ta kuma ban kasa