Da Dumi Dumi

Sojoji sun kubutar da mata 29, yara 25 daga hannun ‘Yan Boko Haram

Rundunar sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram da aka yi wa lakabi Operation lafiya dole tare da hadin gwiwar ‘yan banga sun ce, a ranar Asabar 11 ga Mayu 2019 sun tarwatsa ‘yan Boko Haram a unguwarnin Ma’allasuwa da Yaga a kauyen Munye da ke jihar Borno.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya Kanal Sagir Musa, ya ce a lokacin da dakarun suka isa kauyen duk ‘yan Boko Haram din sun tsere, sun bar mutum 54 da suka yi garkuwa da su.

A cikin wadanda aka bari akwai ‘yan mata 29 da yara maza da mata 25 kuma  duk an kubutar da su.

Share