Search
Subscribe
Sojoji sun tarwatsa masu garkuwa 12 da kwato mutum 15 a dajin Kaduna

Sojin sama sun sa wa’adin gamawa da Boko Haram

Sojoji sun tarwatsa masu garkuwa 12 da kwato mutum 15 a dajin Kaduna

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF),ta ce rundunar ta Operation DIRAN MIKIYA da ke yakar ‘yan bindiga tare da hadin gwiwar rundunar sojoji ta 271 sun tarwatsa masu garkuwa da mutane 12 a dajin Kamuku da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Rundunar sojin ta ce, ta kubutar da mutum 15 da aka yi garkuwa da su don neman kudin fansa.

Daraktan hulda da jama`a na rundunar sojin sama Air Commodore Ibikunle Daramola, ne ya bayyana haka a jiya Talata a Abuja.

Ibikunle Daramola, ya ce kwanan ne aka kaddamar rundunar sojin ta 217 a Birnin Gwari don magance kalubalen tsaron da yake fuskantar yankunan.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin