✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun tarwatsa sansanin ‘yan bindiga 3 da kashe 39 a Zamfara

Runduna ta musamman ta ”Operation Hadarin Daji” wacce ke karkashin rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kashe wani jagoran ‘yan bindiga da ke jihar Zamfara…

Runduna ta musamman ta ”Operation Hadarin Daji” wacce ke karkashin rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar kashe wani jagoran ‘yan bindiga da ke jihar Zamfara da wasu mabiyansa 39, sannan ta tarwatsa sansanonin ‘yan bindigar uku.

Rundunar ta samu nasarar hakan ne a wani sabon atisaye mai suna ”Operation Mushare” mukaddashin jami’in watsa labarai na rundunar Kaftin Ayobami Oni Orisan, ne ya sanar da hakan.

Kaftin Ayobami, ya ce rundunar ta raunata ‘yan bindiga da dama tare kwato makamai da alburusai da babura duk a hannun ‘yan bindigar.

Sojojin sun bayyana cewa yayin wannan arangama, dakarun soji hudu sun rasa rayukansu.

tun a ranar 3 ga watan Octoba, ana fuskantar hare-hare daga ‘yan bindigar, sai aka kara tura dakaru yankin Sunke a karamar hukumar Anka da ke Zamfara, amma sojojin sun yi kokarin dakile hare-haren kuma sun samu nasara a kansu.