✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Faransa 13 sun mutu a hadarin jirgin sama

Gwamnatin kasar Faransa ta sanar da cewa sojojinta 13 da ke aiki da rundunar Barkhane wadda ke yaki da ta’addaci a Mali sun mutu a…

Gwamnatin kasar Faransa ta sanar da cewa sojojinta 13 da ke aiki da rundunar Barkhane wadda ke yaki da ta’addaci a Mali sun mutu a farkon makon nan sakamakon hadarin da suka yi a jirgin sama.

Hadarin ya faru ne yayin da wasu helikwafta biyu suka yi taho-mu-gama lokacin da suke kai wasu hare-hare kan masu tayar da kayar da baya a kasar.

Hadarin ya faru ne a ranar Litinin a cewar wata sanarwa daga ofishin Shugaban Kasar. Fadar Shugaban Faransa ta ce an samu hadarin ne lokacin da jiragen biyu masu saukar ungulu suka yi taho- mu-gama a tsakaninsu.

A shekarar 2013, Faransa ta tura dubban dakarunta zuwa Mali bayan da masu da’awar jihadi suka kwace wasu manyan yankunan Arewacin kasar. An bayyana yankin da hadarin ya faru da yanki mai fama da ayyukan ta’addanci a kasar.

Tuni sojojin Mali suka kwato yankunan amma yankin na ci gaba da fuskantar rashin tsaro, kuma tashe-tashen hankula sun yadu a wasu sassan kasar.

A yanzu akwai sojojin Faransa 4,500 da aka tura Mali da Mauritaniya da Nijar da Burkina Faso da kuma Chadi, don taimaka wa dakarun kasashen a yakin da suke yi da masu tayar da kayar baya.

Shugaba Emmanuel Macron ya  bayyana bakin cikinsa kan hadarin, inda ya nuna kaduwarsa game da hadarin wanda ya hada da hafsoshi shida da wadanda ba hafsoshi ba shida da kuma kofur guda da ke aikin yaki da ’yan ta’adda a Sahel.

Shugaba Macron ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Wadannan sojoji 13 sun rasu da buri daya ne, shi ne kokarin kare mu. Ina taya ’yan uwansu da masoyansu alhini.” Ya kuma bayyana sojojin a matsayin gwarzaye da suka sadaukar da rayuwarsu don kare rayukan jama’a.

A farkon watan nan ne aka kashe wani sojan Faransa Birgediya Ronan Pointeau, bayan da aka dasa bam a kusa da motarsa.

Ministar Tsaro Florence Parly ta ce hadarin ya girgiza rundunar sojin da ma’aikatar tsaro da kasar Faransa baki daya, yayin da ta ce za a kaddamar da bincike a kai domin gano abin da ya yi sanadinsa.

Wannan lamari da ya faru  shi ne mafi muni na asarar rayuka da Faransa ta fuskanta bayan da ta fara shiga tsakani a Mali, kuma mafi muni da sojojin Faransa suka gamu da shi bayan hadarin bama-baman Lebanon na 1983 wanda ya hallaka mutum 58. Kawo yanzu, sojojin Faransa 44 ne suka kwanta dama, tun lokacin da Faransa ta aika rundunarta kasar ta Mali a shekarar 2013.

Mutuwar sojojin ta kara janyo hankulan duniya kan girman matsalar tsaro da kuma gwagwarmayar da ake yi, a kokarin ganin bayan mayaka masu tsattsauran ra’ayi da ayyukansu ya janyo salwantar dubban rayuka.