Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sojojin Najeriya da Kamaru sun kashe mahara 27

Rudunar sojojin hadin gwiwa na Najeriya da Kamaru sun yi nasarar kashe ‘yan Boko Haram 27 a wani samame da suka kaiwa `yan kungiyar, sojojin sun lalata abubuwan hawa tare da kwato makamai masu yawa na maharan  a Borno.

Mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin Najeriya Kanal Sagir Musa ne ya tabbatar da hakan a yau Litinin.

ADVERTISEMENT

Kanal Sagir, ya ce rundunar ta dakile shirin ‘yan Boko Haram a Arewacin Wulgo da Tumbuma, Chikun Gudu da kauyen Bukar Maryam.

 

ADVERTISEMENT