Aminiya

Sojojin Najeriya sun ci galaba kan mayakan Boko Haram – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce kokarin jami’an rundunar sojojin Najeriya yasa aka fara samun zaman lafiya a wuraren da aka fi samun rikici a yankunan kasar.

Shugaba Buhari, ya jaddada cewa a yanzu haka an ci galaba kan mayakan Boko Haram, ba su wani tasiri kamar yadda suke aiwatar da hare-haren su a shekarun baya.

ADVERTISEMENT

Buhari ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da shirin ranar tunawa da mazan jiya da za a yi a shekarar 2020 da kuma gudauniyar gundunmawar tara kudi don ci gaba da gangamin yaki da miyagun aiyuka a jihar.

 

ADVERTISEMENT