✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soke sababbin masarautu: Lauyoyinmu na duba hukuncin kotu – Majalisar Kano

A karon farko Majalisar Dokokin Jihar Kano ta mayar da martani kan hukuncin da wata kotu ta yanke kan dokar da majalisar ta yi ta…

A karon farko Majalisar Dokokin Jihar Kano ta mayar da martani kan hukuncin da wata kotu ta yanke kan dokar da majalisar ta yi ta kirkiro sababbin masarautu hudu a jihar.

Martanin majalisar na zuwa ne kwana biyar bayan hukuncin da kotun ta yanke, sannan a daidai lokacin da ake rahotanni cewa majalisar za ta sake gabatar da kudirin samar da dokar kirkiro masarautun.

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Labaran Abdu Madari ya ce suna ci gaba da tattaunawa da lauyoyinsu da kuma bangaren gwamnati domin samar da matsaya.

Sai dai ya musanta cewa yanke hutun da suka yi na da alaka da batun sababbin masarautun.

“Maganar gaskiya ba abin da ya dawo da mu ke nan ba, saboda shi wannan batu yana gaban kotu kuma lauyoyinmu suna tattaunawa da juna domin cimma matsayar daukaka kara ko akasin haka.

Amma a yanzu ina shaida maka batun da ya dawo da mu daga hutu shi ne na ilimi, ban sani ba ko zama na gaba za a tattauna a kai amma a yanzu babu wannan maganar sam,’’ kamar yadda ya bayyana wa BBC.