✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Solskjaer ya kafa sabon tarihi a kulob din Man United

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya kafa sabon tarihi a shekaranjiya Laraba bayan ya samu nasara a wasanni takwas a waje a jere a…

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya kafa sabon tarihi a shekaranjiya Laraba bayan ya samu nasara a wasanni takwas a waje a jere a gasar rukunin Firimiya.

Kafin wannan lokaci, tsohon kocin kulob din ne Sa Aled Ferguson ya taba lashe wasanni bakwai a jere a waje  ga kulob din amma sai yanzu sabon koci Solskjaer ya kafa sabon tarihi bayan ya lashe wasanni takwas a waje a jere bayan ya lallasa na Crystal Palace da ci 2-0.

Kawo yanzu Solskaer ya yi wasanni 13 ne inda ya samu nasara a wasanni 10 yayin da ya yi kunnen doki a wasanni biyu sannan ya samu rashin nasara a wasa daya bayan da ya karbi jan ragamar kulob din kimanin wata uku da suka wuce.