✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Solskjaer ya zama sabon kocin Man United

A shekaranjiya Laraba kulob din Manchester United da ke Ingila ya bayyana Ole Gunnar Solskjaer a matsayin sabon kocinsa. Solskjaer ya taba buga wa kulob din…

A shekaranjiya Laraba kulob din Manchester United da ke Ingila ya bayyana Ole Gunnar Solskjaer a matsayin sabon kocinsa.

Solskjaer ya taba buga wa kulob din Man United kwallo  a tsakanin 1996 zuwa shekarar 2007.

Sanarwar da kulob din ya fitar a shafin sadarwarsa a shekaranjiyar  mahukunta kulob din sun ce: “Muna sanar da magoya bayan kulob dinmu da daukacin masoya kwallon kafa daga yanzu an zabi Ole Gunnar Solskjaer a matsayin wanda zai gaji Jose Mourinho da kulob din ya kora a ranar Talatar da ta wuce.  Solskjaer zai yi aiki ne har zuwa karshen kakar wasa ta bana kafin kulob din ya dauki kocin dindindin.”

Solskjaear yana Man United da suka samu nasarar lashe kofuna uku ciki har da na Zakarun  Turai a 1999.

Ya horar da kulob din matasa na Manchester United kafin ya koma kasar haihuwarsa Norway a shekarar 2015 inda yanzu haka yake horar da wani kulob a can.

Firayi Ministar Norway a wata takarda da ta fitar, ta nuna farin cikinta game da daukar  Solsjaer dan asalin kasarta a matsayin sabon kocin Manchester United.

Sai dai masana harkar kwallo sun yi hasashen da wuya in Solsjaer zai ya iya kai kulob din United ga tudun mun tsira musamman a wannan lokaci da kulob din yake cikin matsala da sauransu.

Sabon kocin zai iya aiki ne tare da masu taimaka masa da suka hada da Micheal Carrick da Kearan Mckema.

Kawo yanzu Man United tana matsayi na 6 ne a teburin Firimiya na Ingila, kuma Liberpool da ke saman tebur ta ba ta tazarar maki 19 bayan an yi wasanni 17.