Search
Subscribe
‘Son banza’

‘Son banza’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe tare da fatan alheri kuma ana lafiya. A yau na kawo muku wani labari ne a kan ‘son banza’.  Labarin na kunshe da yadda ya kamata Manyan Gobe su zama masu godiya ga iyaye don samun albarka.

Taku: Amina Abdullahi

Akwai wani dan kasuwa mai suna Malam Ali. Yana da mata da ’ya’ya biyu. Suna da rufin asiri daidai gwargwado. Kuma Allah Ya ba su wata kaza wadda take yin kwai kullum. Wani abin mamaki da burgewa da kuma daukar hankali shi ne kazar kwan gwal take yi. Don hadama sai Ali ya rika ganin kazar na bata masa lokaci. Yana so ya samu dukan kwayayen da take yi masa a lokaci guda.

Ran nan sai ya yanke shawarar yanka kazar don ya kwashe dukan kwayayen da ke cikinta.

Washegari, kazar ta yi kwai kamar yadda ta saba. Domin son banza da hadama da gaggawa, sai ya samu wuka mai kaifi, ya kamo kazar ya yanka, ya fede cikinta zai kwaso kwayaye, sai ya yi mamaki da ya ga jini ne cike a cikin kazar, kuma babu wani kwan a cikinta.

Sai aka wayi gari, kwayayen da yake samu kullum a rana sun kare.

Sakamakon son banza da hadama da rashin tawakkali ya sa shi ya fada wani hali na talauci. Kullum talaucin sai karuwa yake yi har ya tsiyace.

Ina fatan Manyan Gobe za su yi amfani da wannan labari don su zama masu godiya musamman ga iyaye. Saboda duk wanda yake da dogon buri idan bai yi hattara ba zai fada ga hallaka.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin