Startimes za ta nishadantar da abokan huldarta da sababbin shirye-shirye a Arewa 24

Ali Nuhu da A’isha Aliyu (Tsamiya), biyu daga cikin ‘yan wasan shirin ‘Abin da Ka yi’ da za a riqa nunawa a Arewa 24.
Ali Nuhu da A’isha Aliyu (Tsamiya), biyu daga cikin ‘yan wasan shirin ‘Abin da Ka yi’ da za a riqa nunawa a Arewa 24.

A kokarinta na nishadantar da abokan huldarta na sashen Hausa kafar labarai ta Startimes ta fara gabatar da sababbin shirye-shirye masu kayatarwa a tashar Talabijin din Tauraro Dan Adam da ta yi zarra a tsakanin tashoshin talabijin, inda ta  bullo da wasu jerin wasannin kwaikwayo da za a rika na nunawa a-kai-a-kai mai suna: “Abin da Ka yi” daga jiya a tashar Arewa 24.

Sababbin wasannin kwaikwayon masu dogon zango da aka yi wa taken: “Abin da Ka yi” za a haska su ne a kowace ranar Alhamis da misalin karfe 1:30 na rana, agogon Afirka; kuma za a iya samun shi a kan zango 138 a turakun Antennna da daukacin tsare-tsaren Startimes din.

Kamar dai yadda Manajan Shirye-Shirye na Startimes, Abosede Adewara, ya ce wasan kwaikwayon na dogon zango zai ta’allaka ne a kan irin wahalhalu ko tsinuwa da bakaken maganganu da wata matar aure ke fuskanta daga surukarta, sakamakon rashin samun haihuwa da ta yi; amma sai dai ta samu farin ciki, bayan da ta  fara soyayya da wani mijin na daban.

“Masu magana da harshen Hausa a Arewacin Najeriya da sauran yankunan kasar, na da damar kallon tashar nishadantarwa da ke haska tsarin zamantakewar al’ummomin yankin Arewa da ke da bambance-bambance da dama ta fuskar al’adu,” inji sanarwar da Startimes ta fitar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mun kara wasu shirye-shirye masu nishadantarwa da dama ga abokan huldarmu; don su samu damar kallon shirye-shirye masu fadakarwa da nishadantarwa; kuma mun yi amanna cewa, bullo da sabon shirin na “Abin da Ka yi” zai kara bunkasa shirye-shiryenmu da suka shafi al’umma kai-tsaye da muke haska wa abokan huldarmu a Nahiyar Afirka baki daya,” inji Babban Manajan Startimes.

ADVERTISEMENT

Wadansu daga cikin fitattun ’yan wasan Hausa da shirin na “Abin da Ka yi” zai rinka haskawa akwai jarumi Ali Nuhu da fitaccen furodusan nan kuma dan wasa, Lawan Ahmed. Sauran sun hada da A’isha Aliyu Tsamiya da Ladidi Fagge, sai kuma Zainab Ishola da sauransu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya